Kungiyar ‘yan sintiri a tashar motar Zuba da ke Abuja, ta kama wani mutum da bindigogi takwas da ya yi niyyar kai su Jihar Kano.
BBC ta rawaito cewa, Jaridar DailyTrust ta ambato shugaban ‘yan sintirin da ke yankin, Yahaya Madaki, yana cewa lamarin ya auku a ranar Laraba.
- Matawalle Ya Amince Da Hukuncin Kisa Kan Masu Garkuwa Da Masu Ba ‘Yan Bindiga Bayanan Sirri
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinan Sadarwa Na Jihar Nasarawa
Ya ce mutumin ya je tashar motar ne da misalin karfe biyu na rana inda yake neman motar da za ta je Kano don bayar da sakon.
Daga nan ne sai ya samu direban da ke lodi zuwa Kano ya mika masa sakon da aka sanya a kwali da kuma lambar wayar mutumin da zai kai wa sakon a Kano.
A cewar jaridar, an caji mutumin naira dubu 10 kudin dakon kayan, kuma nan take ya ciro ya bayar, daga nan ne sai direban motar ya nemi ya ji ko mene ne a cikin kwalin daga nan ne sai mutumin ya nemi ya tsere to amma an kama shi.
Yahaya Madaki ya ce ko da aka bude kwalin an ga bindiga samfurin AK-47 biyar, sai kananan bindigogi uku.
Yanzu haka mutumin na wajen ‘yan sanda inda suke gudanar da bincike a kan lamarin.