Wani matashi mai suna Aled Amusu mai kimanin shekaru 37 a duniya, mazaunin unguwar Yelwan Tsakani da ke Jihar Bauchi, ya fada komar ‘yansanda bisa zarginsa da yi wa diyar udurwarsa ‘yar shekara 9 a duniya fyade.
Wata mata Patience Danladi, ‘yar shekara 36 a duniya ke unguwar Tambari Housing Estate, ita ce ta garzaya caji ofis din ‘yansanda domin shigar da korafi bayan da ta gano wasu lamomi da ba ta saba ganinsu a tattare da diyarta ‘Grace’ ba.
- Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
- Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Bayan da ta fahimci sabbin alamomi a tattare da yarinyar, daga baya ta gano cewa ‘yar nata ta fuskanci cin zarafi da keta mata addi daga wajen Amusu, wanda saurayin uwar ne.
A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, Babban Sufuritendan dansanda, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cewa, cikin gaggawa aka yi tura jami’an ‘yansanda wanda hakan ya kai ga kamo Amusu.
Wakil ya ce an kai yarinyar zuwa babban asibitin Bayara domin likita ya dubata kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi.
A wani labarin kuma, rundunar ‘yansandan ta cika hannunta da wani matashi mai shekara 26 a duniya, Johnson John, mazaunin unguwar Gwallameji, bisa zarginsa da yin safarar wata budurwa ‘yar shekara 19 a duniya, Cecelia Cosmos, zuwa kasar Burkina Faso domin karuwanci.
A cewar ‘yansanda, Johnson ya yaudari Cecelia ne a ranar 12 ga watan Afrilu da sunan zai samar mata da aikin yi a jihar Legas, ta nan ne ya samu damar cimma burinsa na safararta tare da hadin gwiwa da wata mata.
Mahaifiyar Cecelia, wato Rhoda Cosmos, da ke zaune a unguwar Kusu, Yelwa, ita ce ta shigar da rahoton faruwar lamarin ga caji ofis din ‘yansanda a ranar 19 ga Afrilu.
Wakil ya ci gaba da cewa wanda ake zargin ya mika Cecelia ga wata mata da kawai aka iya gano ta da da suna ‘Mama’ inda ita kuma ta yi safarar yarinyar zuwa Burkina Faso domin karuwanci.
Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umarci a gaggauta bin sawun lamarin tare da kamo wanda ake zargi da kokarin cewa yarinyar da aka yi safarar nata.
Rundunar ta ce an kafa kwamiti na kwararru don bin kes din tare da duba shi da sauran kesa-kesan da suka shafi safara domin kara gano wasu abubuwan da neman wanzar da adalci ga wadanda aka cutar.
Wakil ya ce za a tura kes din zuwa sashin kula da manyan laifukan (SCID) domin fadada bincike kuma da zarar aka kammala za gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp