Hukumar Karbar Korafe-Korafen Jama’a Da Yaki Da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta kama sakataren ilimi, shugaban makarantar, da wasu mutane uku bisa zargin tarwatsawa tare da sayar da kayayyaki da suka shafi karafa na makaranta ba bisa ka’ida ba a makarantar firamare da ke Karamar Hukumar Kumbotso. Wadanda ake zargin, da aka kama, an kama su ne a harabar makarantar.
Babban mai ba da rahoto na musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan yaki da cin hanci da rashawa, Malam Sani Umar Sani, wanda ya tabbatar wa da wakilinmu kamen a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce wasu mazauna unguwar da suke motsa jiki da sanyin safiyar ranar Asabar, sun ji waani motsi da hayaniya a tashar Gaidar Makada Special Primary School, Karamar Hukumar Kumbotso.
- Mutum 2 Sun Rasu Yayin Da Bene Ya Rushe Da Su A Kano
- Zabukan Cikin Gida Na Jam’iyyar PDP: Ya Kamata A Kwance Rigiza!
A binciken da aka yi na kurkusa, ya ce sun gano cewa an wargaza kayan makarantar da karafa da aka hada aka kwashe.
“Daya daga cikin mazauna unguwar da ke makotaka da makarantar ya ce da sanyin safiyar ranar Asabar ne ya ga wani mutum tare da wasu yara maza suka nufi ajujuwan makarantar amma jami’in tsaro ya kama su, bayan wani dan bayani aka ba shi damar shiga ajujuwan,” Sani ya bayyana wa manema labarai.
“Bayan haka, magidancin ya ce ya jiyo hayaniya sosai daga ajujuwan, wanda hakan ta sa ya yaynke shawarar duba da kyau, inda a gano cewa ba kawai tarwatsa kayan makarantar ake bay i ba har ma da hada kan wasu karafa domin yin awon gaba da su.
“Daga baya ya sanar da Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Makaranta, Malam AbdulGafar Sanusi Garba, wanda ya ce bai san da wannan aikin ba, yayin da Shugaban Kungiyar Malamai ta Iyaye, Malam Alkassim Muhammad, shi ma aka sanar da shi.
A cewarsu, ba su da wata masaniya kan hakan, domin shugaban makarantar ya kore su kafin cikar wa’adinsu.
Sun ce an sanar da sakataren ilimi na karamar hukumar cewa shugaban makarantar ya sauke su ta wani bangare daban bayan kuma su al’umma ce ta nada su.
“Da muka tuntubi Sakataren shi, ya yi alkawarin duba lamarin amma har yanzu ba mu ji komai daga gare shi ba.
“Ci gaban da muka lura da shi a safiyar yau, mun tambaye su dalilin da ya sa suke wargaza kujerun makarantar da sauran kayayyaki, sai suka ce za a sayar da kayayyakin ne ga mutanen da suke shirya saya bisa ga umarnin hukumar makarantar.
“Ba tare da bata lokaci ba muka dauki bidiyon abubuwan kuma muka sanar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar.”
Wata majiya da ke kusa da hukumar da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce daga cikin wadanda aka kama har da daya daga cikin ‘yan kasuwar, wanda ya sayi karafa da sandunan karfe daga cikin kayayyakin.
Bugu da kari, PUNCH Metro ta samu labarin cewa wadanda ake zargin sun sayar da kayayyakin da aka lalatar da suka haura Naira miliyan 2 akan Naira 250,000.
Har ila yau, an ruwaito cewa Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa ta kaddamar da bincike kan lamarin, domin wadanda aka kama suna hannun ta.
Har ila yau, wata majiya mai tushe a hukumar ta shaida wa wakilinmu cewa, hakan na iya zama dalilin wargaza kayayyakin a mafi yawan makarantun firamare da ke jihar ba bisa ka’ida ba.
Majiyar ta ci gaba da cewa tuni hukumar ta fara aikin samar da manhajoji da za su rika tattara kayan aiki a makarantun da ke fadin jihar tare da sanar da ita idan wani daga cikinsu ya