An tabbatar da mutuwar mutane biyu, tare da ceto wasu biyu bayan da wani bene mai hawa biyu ya rufta da sanyin safiyar Alhamis a yankin Nomansland da ke karamar hukumar Fagge a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na dare, biyo bayan mamakon ruwan sama da ya haifar da ambaliyar ruwa a yankin.
- An Kwaso ‘Yan Nijeriya 167 Da Suka Makale A Libya – NEMA
- Nijeriya Ta Zama Kasa Ta 3 Da Ta Fi Karbar Bashin Bankin Duniya
Benen wanda ke kusa da wata magudanar ruwa, ya taimaka wajen haddasa ambaliyar, wanda ta kai ga rushewar benen.
Kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya tabbatar da cewa an fara aikin ceto nan take bayan faruwar lamarin.
“An ceto mutane biyu da ransu an kai su asibiti, sai dai an samu gawar mutane biyu, ana ci gaba da aikin ceto,” in ji Abdullahi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa rushewar ginin na zuwa ne kwana guda bayan da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, ta bayyana cewa mutane 31 sun mutu, sannan gidaje sama da 5,280 sun lalace sakamakon ambaliyar ruwa a jihar.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya jefa jama’a da dama cikin tsaka mai wuya, inda hukumomi suka gargadi mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su yi taka-tsantsan.