Kotun Hukunta masu aikata Laifukan lalata da Cin Hanci da rashawa ta Jihar Legas da ke Ikeja, ta tasa keyar wani mutum mai suna Onyeka Mbaka zuwa gidan yari bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 15.
Mai shari’a Rahman Oshodi ne ya bayar da umurnin a ci gaba da tsare wanda ake kara bayan an gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhumar da ake masa aikata wannan aika-aika.
- ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Farmaki Ofishin ‘Yansanda A Katsina
- Kotun Ƙolin Nijeriya Ta Tabbatar Da Nasir Idris A Matsayin Gwamnan Jihar Kebbi
Lauyan mai gabatar da kara, Mis Bukola Okeowo, ta shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya bata sunan wacce aka cutar a wani lokaci.
Okeowo ta ce lamarin ya faru ne a lamba 16, titin Moshalasi, a yankin Ilasa na jihar.
Ta ce wanda ake tuhumar ya yi lalata da karamar yarinya ta hayar yi mata fyade.
A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da sashe na 137 na dokar laifuka ta Jihar Legas na shekarar 2015.
Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Bayan kin amsa laifinsa na aikata laifi, mai gabatar da kara ta roki kotu da ta tasa keyarsa zuwa gidan gyaran hali.
Ta kuma shaida wa kotun cewa masu gabatar da kara a shirye suke don yin shari’ar kuma suna da shaidu uku da za su tabbatar da tuhumar da ake yi wa wanda ake kara don haka ta bukaci kotun da ta dage sauraron karar.
Bayan sauraron karar da mai gabatar da kara, Mai shari’a Oshodi ya yi, ya bayar da umarnin a tsare wanda ake karar a gidan yari na Kirikiri.
Ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga Maris, 2024, domin fara shari’ar.