An kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe ‘yan sanda uku a jihar Delta a ranar Lahadin da ta gabata.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Delta, Ari Muhammed Ali, ya ce rundunar ta yi nasarar cafke sauran ‘yan kungiyar.
- ‘Yan Sanda Da ‘Yan Kasuwa Sun Yi Hadin Guiwa Don Kawo Karshen Kwacen Waya A Kano
- ‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Shugaban Jam’iyyar APC A Edo
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Delta ta yi FAllah-wadai da harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa reshen Okpanam na rundunar ‘yan sandan Nijeriya a karamar hukumar Oshimili ta Arewa.
Sakataren gwamnatin jihar, Cif Patrick Ukah ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci ofishin ‘yan sanda na Okpanam domin tantance irin barnar da aka yi a yayin harin da aka kai da sanyin safiyar Lahadi.
Ya bayyana harin da aka kai wa ‘yan sandan da ke ofishin da kuma jami’an tsaro na ‘yan banga Okpanam a matsayin wani mummunan aiki tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
Ukah ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu bata-gari suka kai ba tare da wani dalili ba za su iya kai hari kan al’umar Okpanam da suke zaune lafiya, yana mai cewa abin yana da zafi, ba zato ba tsammani.
Sakaren ya ce kai harin abu ne da ba za a amince da shi ba a jihar, kuma ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an gurfanar da masu laifin.
Ukah ya kuma bayar da tabbacin cewa ba za a sake yin wani yunkuri na biyu ba, kasancewar hukumomin tsaro da suka hada da ‘yan banga na kan gaba wajen fuskantar sabbin kalubalen, yayin da ake ci gaba da bincike kan harin.