Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai ta dage wasan neman tikitin shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League da za a yi yau Talata tsakanin AEK Athens da Dinamo Zagreb, bayan da aka caka wa wani dan kallo wuka a babban birnin kasar Girka, Athen.
Dan kallon wanda dan kasar Girka ne mai shekaru 29, ya mutu bayan artabu tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a wajen filin wasa na AEK Agia Sophia da ke yankin arewacin Athens a yammacin jiya Litinin.
‘Yan sanda a yankin sun ce an jikkata wasu mutum takwas amma an kama mutane 98 wadanda ake zargi da tada tarzoma.
Hukumar kwallon kafa ta Turai ta Uefa ta haramta wa magoya bayan kungiyoyin zuwa kallon wasan zagaye na uku na neman shiga gasar saboda matsalar tsaro.
‘Yan sandan Girka sun ce rikicin ya fara ne mintuna 90 bayan da Dinamo ta Croatia ta kammala atisayen tunkarar wasan a filin wasa na Nea Philadelphia.