Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa an ceto mutane 41 daga cikin waɗanda suka nutse a haɗarin kwale-kwale da ya faru a ƙauyen Kojiyo, cikin ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sakkwato. Sai dai ta tabbatar da cewa mutane huɗu sun rasa rayukansu a wannan mummunan haɗari.
A cewar hukumar, ta kai ziyara ƙauyuka huɗu da lamarin ya shafa, inda ta tantance waɗanda suka tsira da kuma waɗanda suka rasa rayuka. Hakan ya tabbatar da cewa mutum 16 daga cikin fasinjojin da suka shiga jirgin sun tsira daga haɗarin.
- An Gano Karin Gawarwaki 3 Da Jirgin Ruwa Ya Kife Da Fasinjoji 26 A Sokoto
- Sin Ta Kaddamar Da Shirin Gwaji Na Samun Lamunin Waje Ga Bangaren Makamashi Mai Tsafta
Gwamnatin jihar Sakkwato ta sanar da bayar da tallafi ga iyalan waɗanda suka gamu da mummunan iftila’in, ciki har da Naira miliyan 20 da buhunan abinci 100. Haka kuma, gwamnatin ta bayyana shirin raba jiragen ruwa na zamani da rigunan kariya ga al’ummomin da ke zaune a yankunan da suke da ruwa, inda yankin Goronyo zai samu jirage biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp