Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru goma, tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil’adama. A cikin shekarun 10 da suka gabata, Xi Jinping ya yi ta yin karin haske kan ma’anoni masu dimbin yawa, na wannan ra’ayi a wasu muhimman lokuta, kuma a wannan hali da ake ciki na fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda da ya gabata, ya samar da mafita ta kasar Sin ga kasashe daban daban, ta fuskar tunkarar sauye-sauyen duniya, da na zamani, da kuma na tarihi.
A cikin shekaru goma da suka gabata, ba wai kawai an rubuta wannan muhimmin ra’ayi a cikin kundin ka’idojin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da tsarin mulkin kasar ba ne, har ma an rubuta shi cikin takardun muhimman kungiyoyin kasa da kasa, da na shiyya-shiyya irin na MDD sau da dama, inda ya zama muhimmin ra’ayi na al’ummar duniya.
A cikin shekaru 10 da suka gabata kuma, shugaba Xi Jinping ya yi nasarar gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da shirin raya kasa da kasa, da shirin tsaro na duniya, da shirin wayewar kai a duniya, wadanda suka wadatar da ma’ana, da kuma hanyoyin aikawa da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil’adama, kana da inganta tabbatar da wannan muhimmin ra’ayi.
A matsayin wani muhimmin dandali na inganta ra’ayin, ya zuwa yanzu, kasashe 151 da kungiyoyin kasa da kasa 32, sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa game da shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’, fiye da 200 tare da kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)