A ranar 11 ga watan Janairun shekara ta 2023, aka kammala aikin gina babbar hedikwatar cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ko kuma Africa CDC a yankin kudancin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.
Aikin ginin nan, wanda kasar Sin ta hada kai tare da kungiyar tarayyar Afirka (AU) wajen aiwatar da shi, ya kara shaida dadadden zumunci da hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da Afirka, wanda kuma shi ne gagarumin aikin hadin-gwiwar bangarorin biyu da shugaba Xi Jinping ya sha ambatawa.
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”
- MOC:Galibin Manyan Kamfanonin Kasa Da Kasa Suna Son Neman Bunkasuwa A Kasar Sin Cikin Dogon Lokaci
A cewar masana, sabon ginin nan da kasar Sin ta kafa, yana da babbar ma’ana ga inganta kwarewar Afirka a fannonin da suka shafi riga-kafi, da sa ido, da kuma shawo kan cututtuka masu yaduwa.
Gao Jiajia, shi ne shugaban rukunin kula da fasahohin aikin gina hedikwatar Africa CDC. Ya ce, watanni kafin kammala aikin ginin, an samu kwararrun jami’an kiwon lafiya da jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da dama da suka ziyarci wurin, inda suka yaba sosai da ayyukan ginin da aka gudanar cikin sauri kuma masu inganci.
Afirka, nahiya ce mai kasashe masu tasowa da yawa, wadanda ke fuskantar barazanar kiwon lafiya sosai, inda cututtuka masu yaduwa da dama ke ci wa al’ummar su tuwo a kwarya, ciki har da maleriya, da kwalara, da shawara da sauransu. Haka kuma yaduwar annobar numfashi ta COVID-19 na kara haifar da kalubale ga tsarin kiwon lafiyar kasashen Afirka. Hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka na samar da kyakkyawan zarafi ga inganta harkokin kiwon lafiya a nahiyar.
A nasa bangaren, kwararre a dangantakar kasa da kasa, kana babban darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya, Charles Onunaiju ya ce, kyan alkawari cikawa, idan aka dubi abubuwan da kasar Sin ta yi, wato kamar yadda ta yi alkawari, ta baiwa kasashen Afirka alluran riga-kafin cutar COVID-19 bayan da ta samar da su ba tare da bata lokaci ba, kuma ta sanar da aikin gina babbar hedikwatar Africa CDC, daga bisani ta kammala aikin yadda ya kamata, al’amuran dukka da sun shaida cewa, “raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya” ba maganar fatar baki ba ce kadai.
Aikin gina babbar hedikwatar Africa CDC a kasar Habasha, wani bangare ne dake shaida hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya a wadannan shekaru. A shekara ta 1963, kasar Sin ta tura tawagar ma’aikatan lafiyar ta ta farko zuwa kasar Aljeriya, kuma tun daga wancan lokacin, Sin ta fara aikin tura tawagogin ma’aikatan lafiyar ta zuwa kasashen Afirka daban-daban. A yayin da kasashen yammacin Afirka ke kokarin dakile cutar Ebola a shekara ta 2014, Sin ta tura kwararrun likitocinta sama da dubu 1 don taimakawa kasashen yaki da cutar. Daga baya a lokacin yaduwar annobar COVID-19, Sin da Afirka na kara fadada hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi kayan aikin likita, da musayar dabarun yaki da annobar da sauransu.
Kamar yadda shugaban tawagar ma’aikatan lafiya karo na 23 da kasar Sin ta tura zuwa kasar Habasha, Zhang Zhiren ya bayana, ana fatan aikin gina babbar hedikwatar Africa CDC zai zama sabon mafari, inda hadin-gwiwar Sin da Afirka a bangaren kiwon lafiya zai kara habaka yadda ya kamata.
Ban da hadin-gwiwar su a fannin kiwon lafiya, aikin gona shi ma wani fanni ne dake shaida hadin-gwiwa mai karfi tsakanin Sin da Afirka.
Cibiyar nazari da raya albarkatun ruwa ta kasar Uganda, cibiyar misali ce ta fasahohin aikin gona ta zumunci tsakanin kasashen Sin da Uganda, kana sansanin bada misali ne na albarkatun ruwa na hadin-gwiwar kasar Sin da kungiyar FAO da kasar Uganda, inda ake amfani da fasahohin kasar Sin wajen yin ban ruwa. Kwararrun kasar Sin sun isa Uganda a watan Nuwamban shekara ta 2022, inda suka soma aikin hadin-gwiwa a bangaren fasahohin aikin gona na tsawon shekaru uku.
Alkaluman ma’aikatar aikin gona da na kiwon dabbobi da na albarkatun ruwa ta Uganda sun yi nuni da cewa, sama da kashi 70 bisa dari na ‘yan kasar manoma ne. Kuma ayyukan hadin-gwiwar Sin da Uganda sun taimaka sosai wajen raya ayyukan gonar Uganda, har ma za ta koyi dabarun kasar Sin musamman a fannonin da suka shafi samar da isasshen abinci da kawar da matsanancin talauci.
A kasar Burundi kuma, matsalar karancin abinci ta dade da ci wa al’umma tuwo a kwarya. Bisa yarjejeniyar da gwamnatocin Sin da Burundi suka daddale, tun daga watan Agustan shekara ta 2009, kasar Sin ta fara gudanar da aikin hadin-gwiwar kwararrun aikin gona tsakanin ta da Burundi. Kuma a ‘yan shekarun nan, kwararrun kasar Sin sun yi tattaki zuwa jihohi 15 masu noman shinkafa a Burundi, da kai nau’o’in shinkafa 8 da suka dace da yanayin wuraren, al’amarin da ya warware babbar matsalar rashin noman shinkafa a wadannan wurare.
Baya ga samar da tallafi, kasar Sin tana kuma maida hankali sosai wajen inganta kwarewar kasashen Afirka don samar da ci gaba bisa karfinsu. Kasashen Afirka sun dade da fama da matsalolin rashin ci gaban harkokin bada ilimi da karancin kudade na samar da horo ga jama’a. Ita kasar Sin ta dade tana samar da cikakken goyon-baya ga kasashen Afirka a bangaren ilimi, da bada tallafin gina makarantu a kasashen Afirka da dama, da inganta hadin-gwiwar cibiyoyin nazarin kimiyya da fasaha tsakanin Sin da Afirka.
A cewar Paul Frimpong, darektan zartaswa a cibiyar bada shawara kan manufofin Afirka da Sin ta kasar Ghana, kasar Sin ta dade tana nunawa kasashen Afirka goyon-baya wajen inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da samar da dimbin damammakin samun horo, da horas da kwararru a fannoni daban-daban ga Afirka, al’amurran da suka taimaka matuka wajen inganta kwarewar kasashen Afirka wajen samar da ci gaba bisa karfinsu.
A farkon shekarar da muke ciki, wato 2023, ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya ziyarci kasashen Habasha, da Gabon, da Angola, da Benin, da Masar, tare kuma da hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka (AU) da kuma hedikwatar kawancen kasashen Larabawa (AL). Kazalika, bana ce shekara ta 33 a jere, da ministan harkokin wajen Sin ke kai ziyarar aiki ta farko a duk shekara zuwa kasashen Afirka.
A yayin ziyarar sa, minista Qin Gang ya ce, kasar Sin ba za ta yi wani alkawarin da ba za ta iya cikawa ba, kana, ba za ta tilastawa sauran kasashe yin wani abu ba, yana mai cewa ta hakan take kula da dangantakar ta da kasashen Afirka. Yayin da kasar Sin take raya hulda da kasashen Afirka, tana matukar maida hankali kan maufofin mutunta juna, da tabbatar da adalci.
Shi ma a nasa bangaren, wakili na musamman na gwamnatin kasar Sin kan harkokin Afirka, Liu Yuxi ya bayyana cewa, gado gami da ci gaba da yayata zumunci tsakanin Sin da Afirka ya riga ya zama wata kyakkyawar al’ada a cikin harkokin diflomasiyyar kasar Sin.
A halin yanzu, hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka na nuna kuzari da karfi sosai. A shekarar da ta gabata, jimillar kudin cinikayyar bangarorin biyu ta zarce dala biliyan 260, kana, saurin karuwar darajar hajojin da kasar Sin ta shigo da su daga nahiyar Afirka, ta sake zarce saurin karuwar darajar hajojin da ta fitar zuwa kasashen Afirka.
Liu Yuxi ya kara da cewa, a nan gaba, kasar sa za ta ci gaba da kyautata ingancin hadin-gwiwar Sin da Afirka, da habaka cinikayyar da take yi da kasashen Afirka, da fadada hadin-gwiwar su a fannonin da suka shafi kiwon lafiya, da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da raya tattalin arziki irin na zamani da sauransu, a wani kokari na kara samar da goyon-baya ga kasashen Afirka, wajen raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma.
A nasa bangaren kuma, Zhu Weidong, manazarci dake aiki a sashen nazarin harkokin yammacin Asiya da Afirka na cibiyar nazarin ilimin zaman rayuwar al’ummar kasar Sin, ya nuna cewa, hadin-gwiwar Sin da Afirka na da makoma mai haske, kana, zumuncin su zai yaukaka a dogon lokaci.
Ya ce, ko a fannin siyasa, ko a fannin tattalin arziki, ko kuma a fannin mu’amalar al’adu, hadin-gwiwa da cudanya dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka za su ci gaba da karfafa a nan gaba.
A halin yanzu, matsalar basussuka ta fara zama wani babban cikas dake hana ci gaban kasashen Afirka da dama, kuma akwai kasashen yammacin duniya da suka shafawa kasar Sin bakin fenti kan wannan batu, inda a cewar su, wai kasar Sin ta saka wa kasashen Afirka “tarkon bashi”, al’amarin da ya kara bukatar hadin-gwiwar Sin da Afirka, domin kara samun fahimtar juna da kawar da jita-jita. Abun yabawa a nan shi ne, shugabannin kasashen Afirka daban-daban sun fahimci wannan abu sosai, inda a cewar su, Sin ‘yar uwa kana abokiya ta ainihi ce mai aminci gare su.
(Murtala Zhang).