An kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na takwas (CIIE) a yau Litinin, inda aka samu daddale kulla cinikin dalar Amurka biliyan 83.49 a cikin yarjejeniyoyi da aka cimma na shekara guda, wanda adadin da aka samu ya karu da kashi 4.4 cikin dari idan aka kwatanta da na baya kuma ya kai wani sabon matsayi, kamar yadda hukumar kula da bajen kolin na CIIE ta bayyana.
Dandalin baje kolin ya kai fadin murabba’in mita 367,000, inda ya jawo hankulan kamfanoni 4,108 daga kasashe da yankuna 138, lamarin da ya karya tarihin yanayin girma da adadin mahalartan na baya da aka gudanar.
Baje kolin na tsawon kwanaki shida ya kunshi sabbin kayayyaki, da fasahohi da ayyuka 461, ciki har da wasu 201 wadanda aka kaddamar da su karo na farko a duk fadin duniya, wasu 65 da aka kadddamar da su karo na farko a nahiyar Asiya, da wasu 195 da aka kaddamar da su karo na farko a kasar Sin, wadanda suka shafi likitancin kwayoyin halittu, da kayan kere-keren fasaha, da fasahar samar da ci gaba mara gurbata muhalli da ta karancin fitar da hayaki mai dumama yanayi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)













