Ana cikin jimami da alhini a Kenya ranar Alhamis yayin da dubban mutane suka mamaye tituna da filin jirgin sama na Jomo Kenyatta domin tarɓar gawar tsohon jagoran adawa, Raila Odinga, wanda ya rasu a ƙasar Indiya ranar Laraba. Yawan jama’ar da suka taru ya sa hukumomin jiragen sama suka dakatar da dukkan tashi da saukar jirage na ɗan wani lokaci domin dawo da tsari da tabbatar da tsaro.
Hukumar kula da harkokin Jiragen Sama ta Kenya (KCAA) ta bayyana cewa dole ne su dakatar da ayyukan jirage saboda taron jama’a ya toshe hanyoyin shiga da fita a filin jirgin. An kawo gawar Odinga daga kudancin Indiya inda rahotanni suka ce ya rasu sakamakon bugun zuciya. Da farko an shirya kai gawar zuwa majalisar dokokin kasar domin jama’a su yi masa ban kwana, amma saboda taron jama’a ya yi yawa, jami’an tsaro suka karkatar da jerin ayarin zuwa filin wasa na Kasarani, inda dubban mutane suka ci gaba da taruwa.
- Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki
- Kamfanin Sinotruk Na Kasar Sin Ya Kaddamar Da Sabbin Motocin Dakon Kaya A Kenya
Shugaba William Ruto ya ayyana kwanaki bakwai na zaman makoki a faɗin ƙasar domin girmama marigayi Odinga mai shekara 80, tare da umartar a sassauta tutocin ƙasar zuwa rabi. Ya bayyana Odinga a matsayin “jarumin ƙasa da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare dimokuraɗiyya da adalci a Kenya.” Hukumomi sun kafa wuraren zaman makoki a sassa daban-daban na Nairobi domin karɓar dubban masu makoki kafin jana’izar gwamnati da za a gudanar ranar Juma’a.
Talabijin na kasar ya nuna hotunan jama’a a garin Bondo, mahaifar Odinga, inda ake ci gaba da shirin jana’izarsa da za a yi ranar Lahadi. A fadin ƙasar, mutane suna raira waƙoƙin samun ƴanci, suna daga rassan bishiya a matsayin alamar zaman lafiya, suna kuma ɗauke da hotunansa.