Wata kotu da ke zamanta a garin Jos ta yanke wa wani dalibi dan shekara 18, Abubakar Adam, hukuncin daurin watanni tara a gidan gyaran hali, bisa samunsa da laifin satar waya.
Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ya yankewa Adam hukuncin ne bayan kammala shari’ar da aka yi masa bayan ya amsa laifinsa.
- Zan Binciki Bidiyon Dala Na Ganduje -Barista Muhyi
- Gwamnan Sakkwato Ya Nada Manyann Mukaman Gwamnati A Jihar
Bokkos, wanda ya yanke hukuncin daurin watanni tara a gidan yari, ya ba shi zabin tarar N10,000.
Alkalin ya kuma umarci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya N100,000 a matsayin diyya ga wanda ya kai karar.
Ya ce hukuncin zai zama isina ga sauran masu aikata laifi.
Tun da farko, lauyan masu gabatar da kara, Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da kara, Hafizu Hassan, ne ya kai rahoton karar a ranar 20 ga watan Fabrairu a sashen “C”.
Gokwat ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya kutsa cikin dakin wanda ya shigar da karar ya sace wayarsa kirar Samsung da kudinta ya kai N85,000 ya sayar wa wani Abdullahi Gambo kan kudi N13,000.
Ya ce laifin ya saba wa tanadin dokar kundin Final Kod na jihar Filato.