A yau Asabar ne aka kaddamar da fara aiki da na’urar fasahar samar da lantarki ta amfani da iskar CO₂, wadda aka sarrafa a matakin kasuwa, a garin Liupanshui na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, a wani mataki da ya zamo na farko a duniya, na amfani da wannan fasaha domin kasuwanci.
A cewar kamfanin kula da harkokin nukiliya na kasar Sin ko kuma CNNC a takaice, na’urar aikin fasahar mai suna Super Carbon No.1, ta kunshi amfani da dabarun sarrafa narkakkiyar iskar CO₂, wadda ake zafafawa da matsewa, tare da amfani da ita wajen juya injin dake samar da lantarki.
Baya ga wannan aiki, fasahar sarrafa iskar ta CO₂ na da wasu tarin gajiya, da ka iya taimakawa wajen samar da lantarki da hasken rana da sauran fannoni. (Saminu Alhassan)














