• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Fara Aiki Da Sashen Farko Na Layin Dogon Da Sin Ta Gina A Lagos 

by CMG Hausa
3 years ago
Lagos

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jagoranci kaddamar da sashen farko na layin dogon jiragen kasa masu amfani da lantarki, wanda kamfanin kasar Sin ya kammala ginawa a jihar Lagos dake kudancin kasar.

A jiya Talata ne shugaban na Najeriya tare da kusoshin gwamnati, da wakilai daga bangaren kasar Sin, suka kaddamar da layin dogon, wanda shi ne irin sa na farko a yammacin Afirka, da aka aiwatar karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

Tun a shekarar 2010 ne dai kamfanin gine gine na CCECC, ya fara aiwatar da ginin sashen farko na layin dogon mai tsayin kilomita 13 da tashoshi 5, cikin jimillar layin dogon da zai kai kilomita 27 idan an kammala shi baki daya. Kuma da zarar komai ya daidaita, za a rika jigilar fasinjoji sama da 250,000, cikin jiragen kasan da za su yi zirga zirga kan sashen na farko.

Yayin kaddamar da fara amfani da layin dogon, shugaba Buhari, ya jinjinawa karkon aikin, da nagarta, da kuma dadin tafiyar jirgin kasan.

Kaza lika a lokacin kaddamar da fara amfani da sashen na farko, an kuma aza tubalin ginin sashe na 2 mai tsayin kilomita 14.

LABARAI MASU NASABA

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sheda bikin rattaba hannu kan wata sabuwar kwangilar gina sashe na biyu na layin dogo a cikin Legos domin saukaka harkokin sufuri a cikin birnin.

Da yake jawabin maraba, mataimakin gwamnan jihar Legos Femi Hamzat ya ce, “Wannan layin dogo da aka bude a wannan rana ta Talata zai taimaka wajen rage wahalhalu na sufuri da jama’a ke fuskanta a birnin Legos saboda yawan cunkoson ababen hawa, sannan kuma zai bunkasa tattalin arzikin jihar, kana zai saka jihar ta Legos cikin jerin manyan birane na duniya, kamar yadda kuka sani bukatar mutane dai ita ce a gabanmu. A don haka wannan aiki an yi shi ne domin al’ummar jihar Legos. Mai girma shugaban kasa ina so ka ba ni dama kuma domin mika godiya ga dukkannin wadanda suka taimaka wajen tabbatar da wannan aiki musamman ma kai kanka shugaban kasa da kamfanin kasar Sin.”

Shi kuwa da yake nasa jawabin, jakadan kasar Sin wato Mr. Cui Jianchun cewa ya yi, “Zan yi amfani da wannan dama wajen sanar da wasu mahimman batutuwa guda 3 na ci gaba da shugaba Xi ya kirkiro da su domin ci gaban duniya. Na farko muradun raya kasashen duniya, na biyu kuma tabbatar da tsaro a duniya baki daya, sai na uku kuma shirin zuba jari na biliyoyin daloli karkashin shirin tafiya kan gwadabe guda wajen tallafawa tattalin arzikin kasashe wanda ake yi wa lakabi da BRI Initiative, amma dai abin da Sin ta fi fifitawa shi ne kara samuwar hadin kai tsakaninta da kasashen Afrika. Mai girma shugaban kasa ina son na tabbatar maka cewa kudurce-kudurcen ci gaba guda 9 da shugaba Xi ya bujiro da su domin kasashen Afrika, Najeriya za ta amfana da manyan ayyuka har 15 daga kasar Sin. Ina da yakinin cewa muddin kasashen biyu za su yi aiki tare, tabbas kasar Sin za ta iya cimma burinta na kawata biranen Najeriya kamar yadda kasar Sin ta bunkasa a yanzu ta fuskar ababen more rayuwa. Ha’ila yau ina son na kara tabbatar wa Najeriya cewa nan da ’yan shekaru za mu iya cimma muradun nan guda 5 da kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya tanadar wadanda suka kunshi hadin kai wajen bunkasar tattalin arziki, da hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaro da diplomasiyya da yin aiki tare kana da bunkasa harkokin sadarwa tsakanin al`umma.”(Saminu Alhassan, Garba Abdullahi Bagwai)

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal
Daga Birnin Sin

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
Daga Birnin Sin

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza
Daga Birnin Sin

Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 9, 2025
Next Post
Mutum 2 Sun Mutu, 9 Sun Bace Bayan Jirgin Ruwa Ya Nutse Tsakanin Japan Da Koriya Ta Kudu 

Mutum 2 Sun Mutu, 9 Sun Bace Bayan Jirgin Ruwa Ya Nutse Tsakanin Japan Da Koriya Ta Kudu 

LABARAI MASU NASABA

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Lagos

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi

Arewa Ta Daina Zama Ci-Ma Zaune A Tattalin Arziƙi – Gwamnan Bauchi

October 10, 2025
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.