• Leadership Hausa
Wednesday, September 27, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mutum 2 Sun Mutu, 9 Sun Bace Bayan Jirgin Ruwa Ya Nutse Tsakanin Japan Da Koriya Ta Kudu 

by Sadiq
8 months ago
in Labarai
0
Mutum 2 Sun Mutu, 9 Sun Bace Bayan Jirgin Ruwa Ya Nutse Tsakanin Japan Da Koriya Ta Kudu 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ma’aikatan jirgin ruwa biyu ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu tara suka bace a ranar Laraba bayan da jirgin dako ya nutse a cikin ruwa tsakanin kasar Japan da Koriya ta Kudu, in ji hukumomin Japan.

Jami’an tsaron gabar teku na kasashen biyu, tare da jirgin soji da wani jirgin ruwa mai zaman kansa, sun gano 13 daga cikin mutane 22 da ke cikin jirgin Jin Tian, ​​kamar yadda wani jami’in tsaron gabar ruwan Japan ya bayyana.

  • An Fara Aiki Da Sashen Farko Na Layin Dogon Da Sin Ta Gina A Lagos 
  • Da Dumi-Dumi: Dan Takarar Gwamnan Jihar Abia Na Jam’iyyar PDP Ya Rasu

Amma daga baya hukumomin kiwon lafiya na Japan sun tabbatar da cewa biyu daga cikin wadanda aka dawo da su sun mutu, kamar yadda jami’in ya shaida wa AFP.

Ma’aikatan jirgin sun fito ne daga China da Myanmar, amma ba a san takamaiman ainihin wadanda suka mutu, wadanda aka ceto da kuma wadanda suka bace ba, in ji shi.

Ya kara da cewa “Tasoshinmu za su ci gaba da zama a yankin kuma za su ci gaba da gudanar da bincike cikin dare.”

Labarai Masu Nasaba

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

‘Yansandan Jihar Nasarawa Ta Tabbatar Da Sace Wasu Daliba A Jihar

Jin Tian ya aike da sakon kar ta kwana da yammacin ranar Talata daga wani wuri mai tazarar kilomita 110 yamma da tsibirin Danjo mai nisa da kudu maso yammacin Japan.

Jiragen ruwa masu zaman kansu uku ne a yankin kuma sun taimaka wajen daukar biyar daga cikin ma’aikatan jirgin da ya makale, in ji jami’an tsaron gabar tekun Japan.

Tasoshin ruwa da jiragen sama da yawa daga jami’an tsaron gabar tekun Japan da na soja, da kuma masu tsaron gabar tekun Koriya ta Kudu da wani jirgin ruwa mai zaman kansa, sun shiga aikin laluben wadanda suka bace.

Kyaftin din jirgin ya yi amfani da waya, inda ya shaidawa jami’an tsaron gabar tekun Koriya ta Kudu cewa shi da ma’aikatan jirgin na neman dauki daga jirgin da ya nutse a ruwan.

Tags: Gabar TekuHatsariJapanJirgin RuwaKoriya Ta KuduNutsewa
ShareTweetSendShare
Previous Post

An Fara Aiki Da Sashen Farko Na Layin Dogon Da Sin Ta Gina A Lagos 

Next Post

Ministan Harkokin Wajen Argentina: Sin Muhimmiyar Abokiyar Cinikayya Ce Ta Argentina

Related

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe
Labarai

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

5 hours ago
‘Yansanda Sun Dakile Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Kan Wasu Rukunin Gidaje A Katsina
Labarai

‘Yansandan Jihar Nasarawa Ta Tabbatar Da Sace Wasu Daliba A Jihar

7 hours ago
Kungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango
Manyan Labarai

NLC Da TUC Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki Mai Dogon Zango Ranar Talata 3 Ga Oktoba 2023

8 hours ago
2023: Zarge-zargen PDP A Kaina Soki-burutsu Ne Kawai – Gwamnan Gombe
Labarai

Da Dumi-dumi: Kotu Ta Kori Karar Da ADC Ke Yi Kan Gwamnan Gombe

13 hours ago
Cutar Mashako
Labarai

Cutar Mashako: Mutum 453 Sun Mutu, 7,202 Sun Kamu Cikin Watanni 10 A Nijeriya.

15 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga A Zamfara
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Zargin Tattaunawa Da ‘Yan Bindiga A Zamfara

16 hours ago
Next Post
Ministan Harkokin Wajen Argentina: Sin Muhimmiyar Abokiyar Cinikayya Ce Ta Argentina

Ministan Harkokin Wajen Argentina: Sin Muhimmiyar Abokiyar Cinikayya Ce Ta Argentina

LABARAI MASU NASABA

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

September 26, 2023
NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara

NNPP Ta Kai Korafinta Ga Hukumar NJC Kan Kalaman Daya Da Cikin Alkalan Kotun Zaben Kano

September 26, 2023
Duniya

Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya

September 26, 2023
‘Yansanda Sun Dakile Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Kan Wasu Rukunin Gidaje A Katsina

‘Yansandan Jihar Nasarawa Ta Tabbatar Da Sace Wasu Daliba A Jihar

September 26, 2023
JKS

Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar

September 26, 2023
Kungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango

NLC Da TUC Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki Mai Dogon Zango Ranar Talata 3 Ga Oktoba 2023

September 26, 2023
Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

September 26, 2023
Da Alamun SAKA Ba Zai Buga Wasa Biyu Ba Saboda Raunin Da Ya Samu Arteta

Da Alamun SAKA Ba Zai Buga Wasa Biyu Ba Saboda Raunin Da Ya Samu Arteta

September 26, 2023
Kimiyya

Masana Kimiyya Na Kasashen Kenya Da Sin Sun Kaddamar Da Kundin Farko Game Da Nau’ikan Tsirran Da Kenya Ta Wallafa

September 26, 2023
Libya

Me Ya Haifar Da Ambaliya A Libya?

September 26, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.