Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da ɓullar cutar cholera a garin Tureta, ƙaramar hukumar Tureta, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.
Kwamishinan lafiya na jihar ya ce an tura samfurin majinyatan zuwa ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa da ke Jihar Oyo domin tabbatar da cutar. Ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da magunguna ƙyauta tare da taimakon likitoci, inda ya bayyana cewa da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa suna amsawa da magani.
- Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto
Sai dai, mazauna yankin sun yi iƙirarin cewa aƙalla mutane goma ne ke mutuwa a kullum sakamakon annobar, duk da cewa hukumomin lafiya sun rage muhimmancin wannan kididdiga, suna mai cewa har yanzu ana kan bincike kan ainihin dalili da kuma yawan waɗanda abin ya shafa.
Rahotanni sun nuna cewa mata, da ƙananan yara da ƴan gudun hijira ne suka fi kamuwa da cutar. Masana sun alaƙanta ɓullar cutar da yawan mutanen da suka tsere daga hare-haren ƴan bindiga, wadanda yanzu ke cunkushe a makarantu, da kasuwanni da rumfunan kan hanyoyi ba tare da wadatattun wuraren tsafta da kiwon lafiya ba.