Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wani bidiyon da yaɗu a kafafen sada zumunta, inda wasu Sojoji suka nuna rashin jin daɗinsu game da abincin da suke samu daga shugabanninsu.
A bidiyon, an ga wasu daga cikin sojojin suna nuna kayan abinci da ake zargin an aiko musu daga manyan kwamandojinsu, tare da nuna rashin jin daɗi dangane da inganci da yawan kayan abincin.
- Sojoji Sun Daƙile Wani Harin Ta’addanci Tare Da Cafke Wasu Mutum Biyu A Taraba
- Sojoji Sun Kama Jami’an NURTW 2, Da Mai Karɓar Harajin IPOB
Daraktan watsa labaran rundunar Soja na riƙo, Laftanar Kanar Appolonia Anele, ta ce rundunar na ɗaukar lamarin da matuƙar muhimmanci, duk da cewa ba a tantance sahihancin bidiyon da cikakken yanayinsa ba tukuna.
A cewarta, “Saboda haka, COAS, Laftanar Janar Oluyede, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi da cikakken bayani kan lamarin. Kuma a bisa ƙudirinsa na bayyana gaskiya da ɗaukar alhaki, za a fitar da sakamakon binciken ga jama’a idan an kammala.”
Ta ƙara da cewa COAS ya jaddada cewa walwalar Sojoji tana da fifiko a wurinsa tare da ƙarfafa amfani da hanyoyin da suka dace a rundunar wajen miƙa koke-koke maimakon amfani da kafafen da ba su dace ba, domin hakan ya saɓa wa ƙa’idojin soja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp