Wani jirgin ruwan dakon kaya mai rajista a yankin Hong Kong na Sin, ya tashi daga tashar ruwa ta Jiaxing dake lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin a ranar Juma’a, inda ya nufi tashar ruwa ta Zanzibar dake Tanzania da tashar Beira dake Mozambique.
Wannan shi ne karo na farko da jirgin ruwa ya tashi daga Jiaxing ya nufi nahiyar Afrika kai tsaye, inda Jiaxing ta zama tashar ruwa ta biyu a Zhejiang da ta fara irin wannan jigila, bayan tashar Ningbo-Zhoushan.
Jirgin ya tashi ne ranar Juma’a dauke da kimanin kwantainoni 200 da suka mamaye fadin cubic mita kusan 1,000. Galibin abubuwan dake ciki ababen more rayuwa ne dake da nufin tallafawa rayuwar jama’a da ayyukan gine-gine a nahiyar Afrika. Ana sa ran jirgin zai isa tashar ruwa ta Zanzibar cikin kimanin kwanaki 25.
Ana samun habakar cinikayya tsakanin Sin da Afrika a baya bayan nan, inda Zhejiang ke taka muhimmiyar rawa a matsayin lardi mai cinikayya da kasashen waje. Ana sa ran wannan sabuwar hanyar jigila za ta kara karfafa harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Zhejiang da kasashen dake cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.
A cewar hukumomin kula da sufurin teku na lardin, za a rika wannan jigila ne sau daya a wata, inda ake sa ran karuwarta a nan gaba. Haka kuma za ta rage kudin da ake kashewa na jigila da kara habaka hadin gwiwa tsakanin yankin kogin Yangtze da nahiyar Afrika ta fuskar raya ababen more rayuwa da hadin gwiwa a bangaren ayyukan masana’antu da kyautata rayuwar jama’a. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp