Nijeriya ce kasar da ke da kashi 27 cikin 100 na masu dauke da cutar zazzabin cizon sauro a duniya.
Sannna kasar na da kuma kashi 31 na wadanda cutar ke kashewa a duniya, kamar yadda rahoton malaria na duniya na 2023 ya nuna.
- Peng Liyuan Ta Yi Kiran Ci Gaba Da Aiki Da Matasa Wajen Rigakafin Cutar AIDS
- Gwarzon Gwamnan Shekara Ta 2024: Alhaji Abba Kabir Yusuf
Akalla mutum 200,000 ne suka rasu a sanadiyar cutar zazzabin cizon sauro a shekarar da ta wuce.
Kazalika, yara ‘yan kasa da shekara biyar da mata masu ciki ne suka fi saurin kamuwa.
Nijeriya ta karbi allurar rigakafin cutar a watan Oktoba, sannan an fara allurar a ranar Litinin a jihohin Bayelsa da Kebbi.
Daga bisani za a fadada rigakafin zuwa wasu jihohin nan da wasu watanni masu zuwa.