A safiyar yau Talata ne aka fara gudanar da jana’izar shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi mai shekaru 63 a birnin Tabriz, biyo bayan mumunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya rutsa da shi a ranar Litinin.
Hatsarin wanda ya afku cikin yanayi mai hazo sosai a yankin arewa maso yammacin ƙasar Iran, ya kuma ci rayukan wasu manyan jami’ai ciki har da ministan harkokin wajen ƙasar.
- Ya Shiga Hannu Kan Satar Akuya Da Babur A Barikin ‘Yansanda
- Sojojin Iran Za Su Fara Binciken Musababbin Hatsarin Jirgin Da Ya Kashe Raisi
Dubban mutane ne suka cika titunan tare da rakiyar masu gadi, yayin da jami’an ƙasar Iran da manyan baƙi suka ƙarrama Raisi da jawabai da kaɗe-kaɗe da addu’o’i.
Hatsarin dai ya jefa tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin halin rashin tabbas, yayin da ake ƙara samun tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.
Gwamnati ta ayyana kwanaki da dama na zaman makoki a ƙasar, tare da shirya bikin jana’izar ƙarshe a cikin wannan mako.
An fara gudanar da bukukuwan ranar yau Talata a Tabriz da sallar jana’iza da kuma jerin gwano a birnin da hatsarin ya afku.
Yayin da al’ummar ƙasar ke zaman makoki, hukumomi na ci gaba da binciken musabbabin faɗuwar jirgin mai saukar ungulu. Rasuwar shugaba Raisi ta bar wani gagarumin gurbi a fagen siyasar Iran, kuma har yanzu ba a da tabbas kan tasirin shugabancin ƙasar nan gaba da yadda za ta magance kalubalen cikin gida da wajen ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp