Manyan masana’antu mafi rinjaye wajen aiki da fasahar zamani ko “lighthouse factories” wanda aka fi sani da mafi ci gaban masana’antu a duniya. Kuma suke matsayin abin koyi na dunkulewar ayyaukan masana’antu na dijital da intanet, mafi ci gaba, masu aiki da fasahar zamani kuma ke wakiltar masana’antu mara gurbata muhalli.
Kwanan nan ne dandalin tattalin arziki na duniya ya fitar da sabon jerin sunayen “manyan masana’antu mafi rinjaye wajen aiki da fasahar zamani” a hukumance. Inda masana’antun kere-kere 22 suka shiga cikin jerin wadannan manyan masana’antu mafi rinjaye wajen aiki da fasahar zamani na duniya, ciki har da masana’antu 13 daga kasar Sin, wadanda suka hada da masana’antun kera na’urorin wutar lantarki bisa karfin iska, da na makamashin nukiliya, da na kera kayayyakin sufurin jiragen kasa da sauran masana’antu.
Ya zuwa yanzu, jimillar “manyan masana’antu mafi rinjaye wajen aiki da fasahar zamani” a duniya ya karu zuwa 172, kuma yawan kamfanonin kasar Sin ya kai 74. (Mohammed Yahaya)