Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan na bana.
Kwamitin duban wata na ƙasar ya bayyana cewa an ga jinjirin wata a yammacin yau, wanda ke tabbatar da cewa gobe za a fara bukukuwan Sallah.
Wannan na nufin cewa al’ummar Musulmi a Saudiyya za su yi bikin ƙaramar Sallah, domin kammala azumin da suka gudanar a tsawon watan Ramadan.
Hukumomi sun buƙaci jama’a da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da bin dokoki don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.