An gudanar da dandalin tattauna kamfanonin kasar Sin karo na 6 a yau Juma’a, inda aka gabatar da rahoton bunkasuwa mai inganci ta kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiyar kasar na shekarar 2023, inda aka bayyana cewa, wadannan kamfanoni sun ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata.
Rahoton ya nuna cewa, a bangaren yiwa tsarin tattalin arziki kwaskwarima, kamfanonin na kan matsayi mai kyau na zuba jari ga sabbin sana’o’i bisa manyan tsare-tsare, inda saurin karuwar yawan kudaden da suka zuba a wannan fanni ya zarce kashi 20% a cikin shekaru 3 a jere.
A shekarar 2022 kuwa, yawan kudaden da aka kashe a bangaren nazarin sabbin fannonin kimiyya da fasaha, ya karu da kashi 9.8%, kan na makamancin lokaci na bara, kana kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha ya kara inganta. (Amina Xu)