An kaddamar da wani jirgin yaki na rundunar sojin saman kasar Sin samfurin Y-20, a bikin baje kolin sararin samaniya da tsaro na Afirka da aka bude a birnin Pretoria, babban birnin kasar Afirka ta Kudu, a jiya Laraba ranar 18 ga wata. Wannan ne karo na farko da Y-20 ya isa Afirka ta kudu, tare da yin nune-nune a tsaye da ma motsi a bikin baje kolin.
A yayin bikin, Y-20 zai kammala fasahohin sarrafa jirgi 5 a cikin mintuna kusan 10.
- Sin Ta Harba Tagwayen Taurarin Dan Adam Na Tsarin BeiDou
- Yadda Ci Gaban Kasar Sin Ke Amfanar Kasashen Afirka
A ranar bikin bude taron, an jera jiragen yakin Y-20, da dimbin jiragen yaki daga kasashe daban-daban yadda ya kamata a wurin baje kolin, inda Sinawa dake Afirka ta kudu suka garzaya zuwa wurin don daukar hoto tare da wannan jirgi mai daraja da ma’ana daga kasar Sin.
A cikin yan shekarun baya-bayan nan, Y-20 na fita kasashen waje akai-akai don gudanar da ayyuka daban-daban. A shekarar 2022, an nuna jirgin a tsaye a bikin baje kolin sararin samaniya na Austria, tare da tashi zuwa Tonga don gudanar da aikin agaji na jin kai. A shekarar 2024, ya wuce ta kan Dalar Duwatsu tare da jirgin sama guda shida samfurin J-10 na kungiyar August lst ta rundunar sojan saman kasar Sin, kuma ya fara tashinsa na farko a ketare a filin jirgin sama na El Alamein a Masar. (Bilkisu Xin)