A shekara 2015, Sulemana Abdul Samed ya farka daga barci, amma sai wani abu ya bashi mamaki domin ya lura cewa harshensa ya kara girma har ya cika masa baki ta yadda baya iya yin numfashi sosai.
Bayan ya sha magani da ya sayo a wani kemis, wanda ya rage kumburin harshen, dan makarantar babbar sakandaren bai san cewa wannan lamarin zai sauya rayuwarsa gaba daya ba.
- Majalisa Ba Ta Da Hurumin Dakatar Da Shugaban Hukumar Zabe Ta Jiha – Shugaban NBA
- An Nemi Fulani Su Manta Da Bambancin Da Ke Tsakaninsu Don Kubuta Daga Matsalar Tsaro
Kuma daga wancan lokacin zuwa yanzu, Sulemana wanda aka fi sani da sunan Awuche- ya rika kara tsawo har sai da ya kai kafa 9.6 kuma ya ci gaba da kara tsawo.
“Cikin kowane wata uku zuwa wata hudu na ke kara tsawo. Idan ba ka gan ni cikin wata uku ko hudu ba, za ka na kara tsawo,” in ji Awuche yayin da yake hira da wakilin BBC Pidgin Fabour Nunoo.
Tsawon da Awuche ya yi ya sa ya zama wani shahararre a garinsu Gambaga yayin da mazauna garin daga kananansu har zuwa dattawan garin ke kallonsa da ta’ajibi.
“Akwai lokacin da wani dan sanda ya ce nazarce shi da tsawona, saboda haka ya ce zai dauki hoto tare da ni,” kamar yadda ya tuna.
Daga ‘yan siyasa zuwa ga jami’an soji da na ‘yansanda duka suna farin ciki da zarar sunga Awuche, wanda baya ga cewa ya fi kowa tsawo, yana kuma da kyawun mu’amala da sauran jama’a.
“Tsawona ya mayar da ni sahahrarre,”kamar yadda ya shaida wa wakilin BBC wanda ya ziyarci garin na Awuche.
Ya kuma ce da a duk lokacin da ya halarci wani biki, sai mutane a wurin su rika matsowa kusa da shi kuma yana son haka sosai.
Ya kan kuma ba su damar daukar hoto da shi a duk lokacin da suka bukaci haka.
“Likitoci sun ce tsawona na lalura ce mai suna ‘gigantism’ Tsawon da Awuche ya yi ba irin wanda aka saba gani ba ne, domin ko likitoci na kiransa da sunan ‘gigantism’ da turancin Ingilishi.
Sun ce wannan matsala ce da kan sa mutum ya yi tsawon da ya zarce na yawancin mutane.
“Yayin da na je asibitin BMC, sai wani mutum farar fata ya ganni kuma sai ya ce ina da lalurar gigantism.
“Ya kuma ce wani likitan da ya rika duba lafiyarsa ya shaida masa cewa akwai wani abu a cikin kwakwalwarsa da ya kamata a yi masa tiyata domin a cire shi.
Ya ce wannan abin ne ke sa kashinsa ke kara girma da tsawo sosai, kuma ya ce idan ba a cire wannan abin daga kwakwalwarsa ba, ba zai daina tsawo ba kuma wannan kai ya shafar lafiyarsa da ingancin walwala da jin dadin rayuwarsa.
Amma duk da haka Awuche yana fatan yin aure da haihuwar ‘ya’ya, wadanda ya ce yake son ganin yadda za su kasance.
Kuma bai damu da cewa ya fi kowa tsawo ba, domin ya ce haka Allah ya so ya gan shi kenan.
Mun ciro muku daga BBC.