A yau Alhamis ne aka gudanar da babban taron kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha na shekarar 2024, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da gwamnatin birnin Shanghai suka dauki nauyin shiryawa.
Taron na birnin Shanghai mai jigon “Kirkire-kirkire ya samar da sabuwar makoma mai inganci”, a wannan karo ya tattara masana daga sanannun jami’o’i, da cibiyoyin binciken kimiyya da fasaha, da shugabannin kamfanonin kimiyya da fasaha, da cibiyoyin harkokin kudade, don tattauna makomar wasu sana’o’i, kamar fasahohin kwaikwayon tunanin bil adam, da kwayoyin halitta, ta yadda za a tara hikima da karfi, na hanzarta bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko.
Shugaban CMG, Shen Haixiong, ya halarci bikin bude taron tare da ba da jawabi. Inda ya ce a matsayin wata sabuwar kafar watsa labarai mai sauke nauyin dake kan gaba na kasa da kasa, CMG ya yi nasarar fitar da daidaitattun ka’idoji na farko na kasar Sin, wajen yin amfani da fasahohin kwaikwayon tunanin bil adam a fagen kafofin watsa labarai, da kuma “Takardar bunkasa fasahohin kwaikwayon tunanin bil adam”, don inganta ci gaban fasahohin kwaikwayon tunanin bil adam, a fagen kafofin watsa labarai a kasar Sin da ma duniya baki daya. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp