An gudanar da bikin gabatar da littafin “Gwagwarmayar Yaki Da Talauci” cikin harshen Hausa kuma taron karawa juna sani kan harkokin mulki a tsakanin Sin da Nijeriya a birnin Abuja, babban birnin kasar Nijeriya a jiya.
A yayin bikin mahalartar bikin daga Sin da Nijeriya sun gabatar da sabon littafin, inda Sin ta bai wa Nijeriya sabbin littattafan kyauta. Bayan bikin, masanan Sin da Nijeriya sun yi musayar ra’ayoyi da tattaunawa kan kwarewar kasashen wajen gudanar da harkokin mulkin kasashen biyu.
Mahalartar taron sun yi imanin cewa, a halin yanzu, duniya tana fuskantar kalubaloli iri daban daban kamar talauci mai tsanani, da matsalar karancin abinci da sauransu, kasashe masu tasowa ciki har da Nijeriya suna bukatar samun hanyar bunkasuwa da ta dace da yanayinsu.
Nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin rage fatara da ci gaban kasa sun jawo hankalin duniya baki daya, kuma kwarewar da ta samu wajen raya kasa na da muhimmiyar ma’ana. Littafin na “Gwagwarmayar Yaki Da Talauci” ya shaida tunanin shugaba Xi Jinping a fannonin tafiyar da harkokin wurare daban daban na kasar Sin, da yaki da talauci, da sa kaimi ga samun bunkasuwa da sauransu, kuma wadanda suka karanta littafin za su kara sanin dalilin da ya sa jam’iyyar Kwaminis ta Sin ta jagoranci Sin ta zamani wajen samun karfi da wadata da kuma bunkasuwa cikin sauri. (Zainab)