A yau Juma’a 21 ga wata ne aka gudanar da dandalin kasashe masu tasowa, domin tattauna batun zamanantarwa a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin. Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban sashen watsa labarai na kwamitin kolin jam’iyyar Li Shulei, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.
Rahotanni na cewa, a yayin taron, baki daga Sin da kasashen waje sun bayyana yadda turbar da kasar Sin ke bi ta zamanantarwa ta zamo jigon kirkire-kirkire a rubuce da zahiri, cikin salon zamanantarwa na duniya baki daya.
Zamanantarwa bukata ce ta dukkanin bil’adama, don haka kamata ya yi kasashe masu tasowa su yi aiki tare, da budaddiyar zuciya da cikakkiyar himma, su aiwatar da cudanyar mabanbantan sassa, tare da yayata musayar al’adu da koyi da juna. Kazalika, kasashe masu tasowa su karfafa musaya da hadin gwiwa tsakanin masana, su kuma gina hakikanin tsarin raya ilimi na zamani daga kasashe masu tasowa domin moriyarsu.
Ofishin watsa bayanai na majalisar gudanarwar kasar Sin, da cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al’umma, da jami’ar Peking, da karin wasu makarantun ne suka dauki nauyin shirya dandalin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














