A yau Alhamis ne aka gudanar da dandalin kasa da kasa na tattauna batun amfani da na’urori masu basira a fannin watsa labarai na Sin na shekarar 2024 a birnin Wuxi na lardin Jiangsu.
Yayin taron wanda kafar CMG da gwamnatin lardin na Jiangsu suka dauki nauyin gudanarwa, babban daraktan CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi, inda ya ce CMG zai gina sabon dandalin watsa labarai, da hada karfi wajen samar da makoma mai inganci ta wayewar kai na dijital, da ingiza sabon karfi don yayata gina al’umma mai makomar bai daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)