An gudanar da dandalin tattaunawa mai taken “sabuwar alkiblar ci gaban kasar Sin da sabon zarafin ci gaban duniya” a jiya Asabar a birnin Beijing.
Dandali ne wanda ya kasance reshe na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na Hongqiao karo na biyar.
Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, Li Shulei ya halarci dandalin tare da gabatar da jawabi.
Li ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin bikin kaddamar da CIIE, wato baje-kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyar, inda ya shaidawa duniya manufar kasarsa, ta nacewa ga fadada bude kofarta ga kasashen ketare, da nuna sahihancinta na more damammakin ci gaba tare da sassan kasa da kasa, al’amarin dake da babbar ma’ana.
Li ya jaddada cewa, a shekaru goman da suka gabata, kasar Sin a sabon zamanin mu, ta samu ci gaba sosai a yayin da take mu’amala da duniya, inda kuma ta samar da alfanu ga duniya. Ya ce babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, ya kafa sabuwar alkibla ga farfado da al’ummomin kasar Sin baki daya, bisa zamanintarwar kasar mai sigar musamman.
Kaza lika kasar Sin tana fatan inganta cudanya da kasa da kasa, don kyautata hanyoyin zamanantar da kasa. Kana za kuma ta tsaya ga ci gaba da samar da alfanu ga jama’arta, da samar da ci gaba mai inganci, da fadada bude kofarta ga kasashen ketare, da bin tafarkin neman ci gaba cikin lumana, a wani kokari na kara sanya kuzari, da karfin ci gaba ga kasashe daban-daban, gami da kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya. (Murtala Zhang)