An gudanar da gasar harshen Sinanci ta Chinese Bridge, ga daliban sakandare da jami’a, a cibiyar Confucius ta jami’ar Makerere dake Uganda.
Taken gasar na bana, na rukunin daliban jami’a shi ne, “Duniya Guda, Iyali Guda” yayin da na daliban sakandare ya kasance “Kwarewa a Harshen Sinanci”.
Da yake jawabi a wajen gasar da aka yi ranar Asabar, jakadan Sin a Uganda Zhang Lizhong, ya ce gasar ta inganta musayar al’adu tsakanin kasashen biyu, kuma ta zama wani dandali da dalibai ke kulla abota.
Ita kuwa daraktar cibiyar tsara manhajar karatu ta kasar, Grace Baguma, cewa ta yi, ana samun karin malaman dake daukar kwas-kwasan Sinanci, kuma a yanzu, ana koyar da harshen a matakin sakandare.
A cewar Gilbert Gumoshabe, daraktan cibiyar Confucius ta jami’ar Makerere, ta hanyar gasar Chinese Bridge, sun gane cewa dukkan mutane daya ne, babu bambanci. (Fa’iza Mustapha)