Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutane uku wadanda ake zargi da sun kwakule idanun wani yaro mai shekara 16 a duniya domin yin layar bata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwa, inda ya ce cikin mutanen da suka kama har da wani boka, wanda ke amfani da sassan jikin dan Adam domin yin tsafi da su.
- Rikicin Kabilanci: An Fara Binciken Wasu Manyan Sarakuna A Kogi
- Kotu Ta Yi Wa Wadanda Suka Kashe Wani Zabiya Daurin Rai Da Rai A Malawi
Kakakin ya sanar cewa lamarin ya faru a ranar Juma’a ne a Yelwan Bauchi, inda wani mutum mai shekara 32 ya hada baki da wasu mutane biyu, daya mai shekara 38 da kuma wani boka mai shekara 52, inda suka yaudari yaron zuwa wani daji da cewar za su ba shi aiki a wata gona.
Bayan sun isa dajin ne sai suka shake yaron da waya har sai da ya suma, kuma daga nan suka kwakule idanun yaron biyu da wata wuka.
Cikin binciken da ta gabatar a cikin gidan mutumin da ta akw zargi, rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano idanun yaron biyu cikin wata kwarya, da wata jaka cike da maganin gargajiya, da kuma wayar da aka shake yaron da ita.
Kakakin ya ce da zarar sun kammala bincike za su mika wadanda ake zargin gaban kotu, don kuliya manta sabo ya zartar musu da hukuncin da ya dace da su.