ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Gudanar Da Taro Kan “Ci Gaba Mai Inganci Da Nasarorin Da Aka Samu A Jihar Xinjiang” A Taro Na 51 Na Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Na MDD

by CMG Hausa
3 years ago
MDD

An gudanar da taron gefen kasar Sin kan “ci gaba mai inganci da nasarorin da aka samu a jihar Xinjiang” a taro karo na 51 na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD a birnin Bole dake jihar Xinjiang ta kasar.

Yayin taron da aka yi ta kafar bidiyo da kuma ido da ido a jiya, masana da malamai fiye da goma na gida da waje da wasu wakilan jama’ar jihar Xinjiang da wakilan daliban kasashen waje da ke karatu a kasar Sin, sun yi tattaunawa mai zurfi kan sauye-sauyen da aka samu a jihar Xinjiang sakamakon ci gaba mai inganci, da kuma nasarorin da aka samu a fannin kare hakkin bil’adama.

  • Kasar Sin Ta Bankado Karin Shaidu Game Da Kutsen Yanar Gizo Da Amurka Ta Yi Mata

Hussein Ibrahim Morsy, shugaban kwalejin koyar da harsuna da fassara na jami’ar kimiyya da fasaha ta Masar, kuma farfesa a sashen koyar da Sinanci na jami’ar Ain Shams, yana ganin cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan aikin ba da ilmi ga kananan kabilu da yankunan da ‘yan kananan kabilu ke taruwa, kuma ta dauki kwararan matakai na kare hakkin kananan kabilu wajen samun ilimi, da kyautata halin yankunan da ‘yan kananan kabilu ke taruwa da jama’ar dake zaune a yankunan da inganta zaman rayuwar jama’a a yankunan, kuma an samu manyan nasarori.

ADVERTISEMENT

Ye Suya, wata daliba ‘yar Najeriya dake karatu a jami’ar horar da malamai ta Zhejiang, da Ou Jingya, daliba ‘yar kasar Mozambique, sun ziyarci jihar Xinjiang a baya-bayan nan, kuma sun bayyana cewa, hadin kan al’ummar yankin da kokarin da gwamnatin ke yi na karewa da kuma gadon abubuwan tarihi na al’adu da ake gada daga kakanni kakanni, sun burge su kwarai da gaske. A ganinsu, Xinjiang “wuri ne mai cike da karfi”.

Shi kuwa babban darektan cibiyar binciken hakkin dan Adam ta jami’ar koyon dokokin shari’a ta arewa maso yammacin kasar Sin, Chang An cewa ya yi, yadda Amurka da kasashen yammacin duniya ke yayata batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam a jihar Xinjiang, hakika, alama ce ta zahiri ta siyasantar da hakkin bil’adama da amfani da batun don cimma burinsu.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

Kana ya lalata albarkatun jama’ar kasa da kasa a fannin kare hakkin bil’adama don nuna danniya ko babakere, lamarin da ya sabawa manufar ci gaban kare hakkin bil’adama a duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

November 14, 2025
Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

November 14, 2025
Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
Daga Birnin Sin

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

November 14, 2025
Next Post
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Bayyana Imanin Tabbatar Da Samun Ci Gaban Cinikin Waje A Karshen Rabin Shekarar Bana

Ma'aikatar Kasuwancin Sin Ta Bayyana Imanin Tabbatar Da Samun Ci Gaban Cinikin Waje A Karshen Rabin Shekarar Bana

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta

November 14, 2025
Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

ADC Ta Tsara Ka’idojin Da Shugabanninta Za Su Bi Don Tunkarar Zaben 2027

November 14, 2025

Rikicin PDP: Fiye Da Wakilai 3,000 Ne Za Su Raba Gardama A Babban Taron Jam’iyyar

November 14, 2025
Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

Kasar Sin Ta Kara Azamar Kirkiro Da Fasahar Sadarwar 6G

November 14, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 14, 2025
Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

November 14, 2025
Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

November 14, 2025
Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

November 14, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.