Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya jagorancin taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO a birnin Tianjin na Sin.
A cikin jawabin da ya gabatar, Wang ya ce, cudanyar mabambantan bangarori a duniya da dunkulewar tattalin arzikin duniya na ci gaba da samun karbuwa, haka kuma hadin gwiwar kasashe masu tasowa na kara habaka. A sa’i daya kuma, ana fuskantar kalubalen babakere da fin karfi, har manufar kariyar cinikayya da barkewar rikice-rikice na kunno kai. Yana cewa dole ne kasashe mambobin SCO su kai ga matsaya daya kan karfafa hadin gwiwa karkashin wannan yanayi.
- Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili
- ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Wang ya kuma bayar da shawarwari guda 5 game da bunkasuwar SCO a nan gaba, ta farko nace wa akidar ruhin Shanghai, ta biyu hadin kai da tinkarar kalubaloli da matsaloli tare don tabbatar da tsaron kasashen baki daya. Ta uku kuma, hada hannu da cin moriya tare. Ta hudu, kara zumuncin makwabtaka da neman makoma mai haske ta bai daya. Sai ta biyar, nacewa ga tabbatar da adalci da daidaito da tsare gaskiya.
An yi wannan taro ne da burin share fagen taron koli na SCO da za a yi nan gaba a birnin, inda aka kulla yarjejeniyoyi kan daftarin samun ci gaba nan da shekaru 10 masu zuwa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp