ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Abubakar Ya Fice Daga PDP, Duba Dalili

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da bayyana dalilan sa da suka shafi saɓani da karkacewar jam’iyyar daga ainihin manufofinta na kafuwa.

A wata wasiƙar da aka sanya wa kwanan wata 14 ga Yuli, 2025, wacce ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Jada 1, a ƙaramar hukumar Jada ta jihar Adamawa, Atiku ya rubuta cewa: “Ina rubuto wannan wasiƙar ne don sanar da ku hukuncin ficewata daga jam’iyyar PDP daga wannan rana.”

  • Ina Cike Da Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari — Atiku
  • Zan Yaƙi Duk Wanda Ya Yi Sata Idan Na Zama Shugaban Ƙasa — Atiku

Atiku, wanda ya kasance mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007 tare da kasancewa ɗan takarar shugaban ƙasa sau biyu a ƙarƙashin PDP, ya bayyana cewa wannan mataki yana da matuƙar nauyi da raɗaɗi a zuciyarsa. “A matsayin ɗaya daga cikin waɗanda  suka kafa wannan jam’iyya mai daraja, ficewa daga cikinta abu ne mai matuƙar raɗaɗi gare ni.”

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa akwai saɓani da aka gaza sulhu tsakaninsa da jam’iyyar, inda ya bayyana cewa PDP ta gushe daga ainihin hanyarta. “Na yanke shawarar ficewa ne saboda yadda jam’iyyar ke tafiya yanzu ya sha bamban da manufofin da muka tsaya a kai tun farko.”

Atiku ya kammala wasikar da godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da goyon bayan da ya samu tsawon shekarun da ya kwashe a cikinta. “Ina fatan jam’iyya da shugabanninta za su yi nasara a gaba. Na gode bisa damar da aka ba ni.”

LABARAI MASU NASABA

Ɓarayi Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano

Masana Sun Goyi Bayan Amfani Da AI Wajen Tantance Rajistar Masu Zaɓe

An tabbatar da karɓar wasiƙar ficewar a ofishin gundumar PDP ranar 14 ga Yuli, 2025, tare da sanya hannu da hatimin karɓa daga wani wakili mai suna Hamman Jada Abubakar.

Atiku
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Masana Sun Goyi Bayan Amfani Da AI Wajen Tantance Rajistar Masu Zaɓe
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Masu Amfani Da Wema Bank Za Su Duba Cancantar Samun Tallafin 50,000
  • Abubakar Sulaiman
    Ku Daina Amfani Da Kotu Wajen Hana Mu Takara A 2027 ADC Ga APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴansanda Sun Kuɓutar Da Shugaban APC Na Rogo Bayan Shafe Kwana 68 A Hannun Masu Garkuwa

MASU ALAKA

Ɓarayi Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano
Manyan Labarai

Ɓarayi Sun Kwance Fanka 25 A Wani Masallaci A Kano

November 9, 2026
Masana Sun Goyi Bayan Amfani Da AI Wajen Tantance Rajistar Masu Zaɓe
Manyan Labarai

Masana Sun Goyi Bayan Amfani Da AI Wajen Tantance Rajistar Masu Zaɓe

November 9, 2026
Talauci Ne Ke Tilasta Wa Almajirai Yin Bara A Tituna — Sarkin Musulmi
Manyan Labarai

Talauci Ne Ke Tilasta Wa Almajirai Yin Bara A Tituna — Sarkin Musulmi

November 9, 2026
Next Post
An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano

An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

November 9, 2026
’Yansanda Sun Kai Samame Maɓoyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane Biyu a Sakkwato

’Yansanda Sun Kai Samame Maɓoyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane Biyu a Sakkwato

November 9, 2026
Sin Ta Kara Watanni Biyu Kan Waadin Dakatar Da Daukar Matakan Hana Fitar Da Wasu Hajoji Ga Wasu Sassan Amurka 16

Sin Ta Kara Watanni Biyu Kan Waadin Dakatar Da Daukar Matakan Hana Fitar Da Wasu Hajoji Ga Wasu Sassan Amurka 16

November 9, 2026
Kotu Ta Wa Malamin Islamiyyan Da Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyade Daurin Rai Da Rai

Bayan Shekaru Biyar, Kotu Ta Wanke Mutumin Da Ake Zargi Da Kashe Matarsa A Kano

November 9, 2026
Sin Ta Jinjinawa Gwamnatin Papua New Guinea Bisa Matakin Rufe Ofishin Raya Tattalin Arziki Na Taipei Dake Kasar

Sin Ta Jinjinawa Gwamnatin Papua New Guinea Bisa Matakin Rufe Ofishin Raya Tattalin Arziki Na Taipei Dake Kasar

November 9, 2026
Takardun Naira

Tallafin Naira Dubu 50: Su Wane Ne Za Su Amfana Da Shirin?

November 9, 2026
Yadda Matakin Hadin Gwiwar Makamashi Na Sin Da Afirka Ya Bambanta Da Na Kasashen Yamma

Yadda Matakin Hadin Gwiwar Makamashi Na Sin Da Afirka Ya Bambanta Da Na Kasashen Yamma

November 9, 2026
ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya

ADC Ta Yi Hasashen Kayar Da Tinubu A 2027, Ta Zargi APC Da Kai Wa ’Yan Adawa Hari

November 9, 2026
CIIE: Dandalin samun wadata

CIIE: Dandalin samun wadata

November 9, 2026
Daga Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Jakadu Uku Bayan Tsawon Shekara 2 Ana Jira

SERAP Ta Bukaci Gwamnati Ta Yi Cikakken Bayani Kan Rabon Tallafin N50,000

November 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.