A ranar Litinin ne aka gudanar da taron tattaunawa a tsakanin kafofin watsa labaru na kasar Sin da na kasashen Larabawa, mai taken “Dangantakar dake tsakanin Sin mai kama sabon tafarki da sauran kasashen duniya”, a kasar Saudiyya cikin nasara, taron da babban rukunin gidajen rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya kira, tare da daukar nauyin gudanarwa, da hadin gwiwar wasu manyan kafofin watsa labaru na kasashen Larabawa fiye da 30 da suka halarci taron.
Jami’an gwamnatocin kasashen Saudiyya, da Masar, da Algeria, da Palesdinu da Yemen, da shugabannin kafofin watsa labaru mahalarta taron tattaunawar, da wakilan hukumomin da abin ya shafa, da jakadan Sin mai kula da harkokin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa, da sauran sassa fiye da dari daya, sun yi musayar ra’ayoyi kan sabuwar dama da kasar Sin mai kama sabon tafarki, da kasashen Larabawa suke fuskanta a sabon zamani, da muhimmiyar ma’anar raya makomar bai daya ta bangarorin 2, da kuma yadda za a sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, ta hanyar hadin gwiwar kafofin watsa labaru na Sin da kasashen Larabawa.
Kaza lika mahalarta taron tattaunawar sun amince da cewa, a gun babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta Sin karo na 20 da ya gabata, an fitar da taswirar bunkasuwar Sin a nan gaba, wadda ta samar da fasahohi ga kasashen Larabawa a wannan fanni, kana hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru na Sin da na kasashen Larabawa, zai taimaka wajen raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)