Yayin da ake gudanar da taron shugabannin kasashe mambobin BRICS karo na 16, an gudunar da taron tattaunawar kafofin watsa labarai na Kazan na kasashen BRICS yau Laraba, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da kamfanin talabijin da rediyo na kasar Rasha suka gudanar tare.
Shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, kafofin watsa labarai na kasashen BRICS, sun dade suna dauke da ruhin bude kofa, da hadin gwiwa don cin nasara tare, kuma suna dukufa wajen zama masu yada dabi’un bai daya, masu kiyaye nau’ikan wayewar kai, da kuma jagorantar hadin gwiwar al’adu.
Shen Haixiong ya kuma gabatar da shawarwari guda uku. Da farko ya ce akwai bukatar fitar da muryoyin bai daya, don ba da labarai masu burgewa, game da inganta zamanantarwa tare. Na biyu, a inganta ci gaba tare, don kara karfin hadin gwiwar bangarori daban daban. Na uku, a yada dabi’un bai daya, da kuma inganta karfin jagorantar ra’ayin al’ummun kasa da kasa. (Safiyah Ma)