Jumma’ar nan ce, a birnin San Francisco na kasar Amurka, aka gudanar da taron tattaunawar musayar al’adu da sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Amurka, wanda babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kungiyar musayar daliban kasar Sin dake Amurka suka shirya a birnin San Francisco na Amurka, domin tattauna dangantakar abokantakar da ta yadu daga zuriya zuwa zuriya tsakanin al’ummomin Sinawa da Amurkawa, da kara dankon zumunci da inganta tattaunawa tsakaninsu.
Shugaban CMG Shen Haixiong da Sarah Lande, wata abokiya ’yar Amurka kuma tsohuwar mamba a kwamitin kula da sada zumunta ta jihar Iowa a kasar Amurka, da Elyn MacInnis, masanin tarihi da al’adu na unguwar Kuliang dake birnin Fuzhou na kasar Sin, duk sun halarci taron tare da gabatar da jawabai. (Ibrahim)