Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya bayyana cewa, an gudanar da zaben kananan hukumomin jihar su 23 lami lafiya kuma cikin kwanciyar hankali.
Gwamna Sani ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ya kada kuri’a a mazabarsa da ke makarantar Firamare ta Kawo a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.
- Gwamna Jigawa Ya Dakatar da Kwamishinansa Kan Zargin Aikata Lalata Da Matar Aure
- Gwamnatin Kebbi Ta Kafa Kwamitin Kwato Kuɗaɗen Da Aka Sace A Asusun Marayun Jihar
Gwamnan ya bayyana cewa, bayan rangadi a wasu sassan kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar, an tabbatar da cewa, ana gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da wani hargitsi ba.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin zaben kananan hukumomi, inda ya ce, “don haka, aka bai wa duk jam’iyyu damar gudanar da yakin neman zabe kuma kowa ya fito ya kada kuri’a ba tare da tashin hankali ko tsangwama ba”.
Sai dai Gwamnan ya nuna fata da karfin gwiwar cewa, APC za ta lashe dukkanin kujerun shugabancin kananan hukumomin jihar.
A karshe, Gwamnan, ya yi kira ga sauran jam’iyyun adawa da ke cikin zaben, su yi imanin cewa, a zabe akwai nasara kuma akwai faduwa. Don haka, dole mu amsa kaddara a matsayinmu na masu mulkin Dimokuradiyya.