Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta ce, wani jami’inta mai suna Insifekta Abel Isah Dickson ya mutu bayan rashin jituwa da hatsaniya da ta shiga tsakaninsu da wasu abokan aikinsa guda biyu kan wasu kayayyakin da aka amso daga wajen wani da ake zargi a Jihar Sokoto.Ā
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce, kayayyakin sun hada da magunguna da wasu kudade.
EFCC ta bayyana sunayen jami’an biyu sun hada da Mataimakin Sufuritendan hukumar EFCC, Apata Oluwaseun Odunayo da Insifekta na hukumar EFCC, Ogbuji Titu Tochukwu, wadanda tunin aka cafke su tare da gurfanar da su a kotu a jihar Sokoto kan zargin kisan kai.
Uwujaren ya kuma ce, shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, za su tabbatar an wanzar da adalci wajen hukunta jami’an, ya ce, an dakatar da jami’an biyu yayin da bincike ke cigaba da gudana.
Ya ce, Bawa ya sha alwashin ba zai lamunci wani dabi’a ta rashin da’a ba, “Shugabanmu, Abdulrasheed Bawa, ya kadu da wannan lamarin kuma ya jajantawa iyalan jami’in da ya rasa ransa.
āYa kuma tabbatar da cewa jami’an da suka yi sanadiyyar rasa jami’in namu tabbas za su fuskanci hukunci har sai adalci ya wanzu.”
Kazalika, Bawa ya gargadi jami’ansa da su daina kokarin kauce wa ka’idar aiki da koyarwar da aka musu. Ya nuna cewa ba za su lamunci rashin bin matakan aiki da koyarwar da aka yi wa jami’an ba.
“A halin da ake ciki, an bisne jami’in namu da ya mutu a ranar Asabar 13 ga watan Mayun 2023 a Jos ta jihar Filato.”
“Matashin jami’in namu ya mutu ne a ranar 7 ga watan Mayun 2023 a asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu DanFodiyo da ke Sokoto yayin da ke amsar kulawar Likitoci bayan raunukan da ya samu kwanaki biyu kafin nan a wani hatsaniyar da ya barke tsakaninsa da wasu jami’anmu biyu masu suna Apata Oluwaseun Odunayo da Insifekta Ogbuji Titu Tochukwu.
“Sun samu rashin jituwar ne kan wasu tsarin ajiye wasu kaya mallakin wani da ake zargi da ke tsare, hakan ya kai su ga yin fada, lamarin da hukumar nan ta yi tir da shi.
“Jami’an biyu an dakatar da su kuma an mikasu ga ‘yansandan Nijeriya inda suka gurfanar da su.
“An shigar da su kara ne kan zarge-zargen guda biyu da suka hada da hada baki wajen aikata kisan gilla a gaban babban Kotun Majistire, Gwiwa da ke Sokoto.”
āLaifukan biyun su na da hukunci a karkashin sashe na 60 da na 191 na dokar final kod ta Jihar Sokoto, 2019.
“Ba tare da nuna kyama ga binciken ‘yan sanda ba, za su kuma fuskanci karin matakan ladabtarwa bisa ka’idojin ma’aikatan hukumar.”