A ranar Litinin din da ta gabata ne aka tasa keyar wasu mutum uku da ake zargi da laifin kisa da kuma yunkurin yin wani kisan kai zuwa cibiyar gyaran hali ta Kirikiri da ke Legas.
Wadanda ake tuhumar, Mukaila Nofiu, Wasiu Rasheed da Hassan Kazeem, an gurfanar da su a gaban wata kotun Majistare ta Yaba bisa zargin kashe wani Alade Bello da kuma yunkurin kashe Lasisi Sikiru wanda har yanzu yake jinya.
An gurfanar da su a gaban Majistare O.Y. Adefope akan tuhume-tuhume uku na kisan kai da kuma yunkurin wamni kisan kan.
A cewar mai gabatar da kara, Haruna Magaji, wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 14 ga Afrilu, 2023, a kauyen Igbolodo, daura da Ketu, Omu Road, Legas da misalin karfe 2:46 na rana.
Magaji ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun yi amfani da katako da ita ce wajen lakadawa mamacin duka har lahira kuma sun yi yunkurin kashe daya amma ba su yi nasara ba.
Ya kara da cewa laifukan sun ci karo da sashe na 233 da 230 na dokokin laifuka na jihar Legas ta Nijeriya, a 2015.