Da za mu koma baya kadan, cikin wata kididdiga da aka gudanar ran 25 ga Watan Mac din Shekarar 2023, an hakaito cewa, jihar Kano ta lankwame bashin gida har na kimanin naira biliyan dari da ashirin da biyar, da miliyan dari da tamanin da shida, da dubu dari shida da sittin da biyu da mitsamitsai (N 125,186,662,228.72).
A daya hannun, ta hadiyi basuka daga kasashen ketare har na kimanin dalar Amurka miliyan dari da tara, da dubu dari hudu da ashirin da biyu da mitsamitsai ($109,422,176.85).
- Na Yi Mamakin Ganawar Antony Blinken Da Tinubu -Atiku
- An Tura Budurwar Da Ta Ci Zarafin Dan Sanda Gidan Yari
Kamar yadda a wannan dandali akan gabatar da wasu daga nau’ikan basukan gida da daji da wata jiha daga jihohin wannan Kasa ta ciwowa ‘yan jiha, karkashin ikon da gwamna ke da shi karkashin Kundin Tsarin Mulkin Kasa, tare da yunkurin warware zare da abawa ta wasu fuskoki, haka ita ma jihar Kano za ta amshi irin wancan fidiya ko hisabi bakin gwargwado, babban gurinmu da sauran masu kishin kasa bai wuce a yi gaggawar tashi a gyara ba tun gabanin lamarin ciwo basukan bai yi irin rikar da zai gagari kundila ba!!!. Gyara kayanka ba shi zamo sauke mu raba ta kowace fuska–fahimta fuska.
Cikin 18 ga Watan Mac na Shekarar 2022, gwamnatin jihar Kano karkashin jagoranci gwamna Ganduje, ta samu sahalewar ‘yan majalisar jiha, wajen ranto bashin zunzurutun kudade har na kimanin naira miliyan dubu goma (N 10bn), don sanya na’urorin CCTB a cikin birnin Kano.
Cikin Watan Satumbar Shekarar 2022, gwamnatin dai ta Gandujiyya, ta sake ranto bashin zunzurutun kudade har na kimanin naira miliyan dubu hudu (N 4bn), don kammala kason karshe na aikin wutar Challawa-Goje da kuma Tiga. Alhali tun da fari ‘yan majalisun, sun sahalewar gwamna karbar bashin naira miliyan dubu goma (N 10bn) don yin wannan aikin wuta da aka ambata, sai dai gwamna Ganduje, ya ja dunga tare da cewa, kudaden, sun yi kadan ba za su isa a kammala aikin ba. Sai hakan ya sanya ‘yan majalisun suka kara yi masa tagomashin zuwa ya kara kandamo bashin na naira miliyan dubu 4, sai a jibga bisa waccan naira miliyan dubu 10 ta fari, jumla, an fitar da naira miliyan dubu goma 14 ke nan da sunan aikin wutar! Zuwa yanzu, shin, an kammala aikin wutar ne? Ko ba a kammala ba? Idan an kammala, shin, an hada tashar wutar ne da gidajen jama’a ne koko da kamfanoni ne aka hada ta?.
Da daman aiyuka da Baba Ganduje ya gada daga wasu gwamnoni da suka shude, mutane irinsu Kwankwaso da Shekarau, sai a iske ya kammala su nan da nan. To me ya hana hanzarta kammala aikin wutar, ya zamana ta fara aiki ka’in da na’in tun gabanin saukarsa daga kujerar iko? Cikin aiyukan da ya kammala, wanne ne zai kere irin wannan aikin wuta wajen tsamo jihar ta Kano daga gabar bashin da aka riginginar da ita a bakinsa?. Ba ya ga shi ne irin aikin da zai taimaka wajen sauke nauyin basukan da ya rantowa al’umar ta Kano, shin, cikin aiyukan da ya hatama, wane aikin ne zai samarwa da miliyoyin mutanen Kano aiyukan-yi, sama da samar da manyan tashoshin wutar lantarki a jihar? Dubban daruruwan mutane nawa ne suka rasa aiyukan-yi a Kano, sanadiyyar kamfar wutar lantarki da shugabannin Kasar suka cilla ta ciki?.
Na’am, sanya na’urorin CCTB a jihar Kano na da gayar alfanu ta fuskar bunkasar sha’anin tsaro, to amma, da sanya waccan na’ura da kuma samar da dubban aiyukan-yi ga dubban matasan jihar ta Kano wanne ya fi alfanu? Bugu da kari, cikin biyun, wanne zai fi gudan taka muhimmiyar rawa zuwa ga kassara bashin da yai wa jihar katutu?. Sai aka wayigari gwamna a Kasar ta Najeriyar yau, kan hada kai ne kurum da ‘yan majalisun jiha ya ciwo bashi iya bashi na adadin makudan kudaden da suka so. Bayan ciwo bashin, sai kuma a turbuda kudaden a inda oga gwamna yai ra’ayi! Batun, shin, anya an sanya wadancan kudade ne a inda za su haihu a rabu da annobar basukan da shugabanni suka jefa Kasar ciki?, duka wannan ba wani abin tambaya ne ba ko tuhuma!!!.
Cikin Watan Mac na Shekarar 2021, wadannan dai ‘yan majalisun na Kano, sun kara sahalewar gwamna Ganduje zuwa sake cin wani bashi daga gida har na kimanin naira miliyan dubu hamsin (N 50bn), don samun sukunin gabatar da wasu manyan aiyuka irinsu, gina hanyoyin Janguza-Durum-Kabo da kuma Karaye. Da kuma gina hanyoyin biranen masarautun Kano irinsu masarautar Rano, Bichi, Gaya da kuma Karaye.
Haka nan, cikin Watan Mac din Shekarar 2020, majalisar jihar ta Kano, ta sahalewar mai girma gwamna ciwo bashin zunzurun kudade har kimanin naira miliyan dubu hamsin (N 50bn), don samar da aiyukan more rayuwa ga jama’ar Kano. Misali, yin gine-gine, samar da ruwn sha, samar da wutar lantarki da kuma samar da ababen sufuri. Wannan dogon nazari game da bashi da ake kan tattauna shi tsawon Satika, ba wai yana yin adawa ne ba da samar da hanyoyi, samar da gadoji da sauran gine-gine, ko alama, yana dai so ne a sanya kwarya a gurbinta tamkar yadda masana tattalin arziki suka wassafa. Sabanin haka, dole ne akwai ranar da-nasani na tafe, wadda ita ce wannan rubutu ke jan hankulan jama’a don kaucewa wancan yanayi da ake fuskanta na salallami ranar da hakan ba zai amfanar ba.
Shin, mene ne banbancin ciwo basukan da gwamnatin El-Rufa’i ta yi, da kuma na gwamnatin Ganduje? Gaskiyar zance, kusan a ce daukacin gwamnoni a wannan Kasa tunaninsu na yin kwabo da kwabo ne, ta fuskar nutsar da al’umarsu cikin rijiyar bashi, tare da nuna hali na ko’in kula, wajen yunkurin tsamar da jama’ar jihohin nasu daga muguwar talalar da irin wadancan basuka ke yi wa mabanbantan al’umomin Duniya tsawon lokaci.
Sai a ga duk harkar da za ta agaza zuwa ga rage dandazon basukan a Kano, gwamnati na yi mata rikon sakainar kashi ne! Na’am, harkar sufuri na daga ababen da ke a kan gaba wajen rikito tsirin da shurin bashi ke da shi cikin kowace Kasa. Me mutumin Kano zai ce game da manufar gwamnatin ta Ganduje ga batun sufuri? Yanzu mutum zai hada harkar sufuri da gwamnati ta samar tsakanin na Kano da na Lagos, wajen kara samar da kudaden shiga ga jiha, don biyan bashi da kuma samar da wasu muhimman aiyuka?. Manyan manyan motoci da gwamnatin Kano ta sayo, wane mamakon kudade ne suke samarwa da gwamnati, wanda kowa zai ce gara da aka saye su?. Maganar ruwan sha, shin, yanzu da akwai kyakkyawan tsarin samar da wadataccen ruwan sha a Kano? Wa zai iya kididdige irin biliyoyin kudaden da gwamnati za ta rika yin habzi da su a duk Wata da sunan kudaden shiga idan aka infants harkar? Shin, akwai wani lokaci da jama’ar Kano suka tsunduma cikin kamfar ruwan sha sama da yanzu? Idan babu, ke nan ai yanzu ne lokacin da gwamnati za ta ingiza biliyoyin kudade cikin harkar, don samun kudaden shiga, wadanda da sune ake biyan bashi tare da gabatar da managartan aiyuka a Kasa. Idan ba yanzu ba ne, to sai zuwa yaushe ne?
Sai aka wayigari, sahihan hanyoyin da gwamnati za ta bi don biyan makudan basukan da ta hadiya daga gida da waje, sun yi gabas, ita kuma gwamnatin ta yi yamma! Sai aka tafi ne kawai zuwa ga kawata cikin birane tamkar irin yadda gwamnatin Nasiru ke yi dare da rana. Ba a damu da gina DAN’ADAM ba, kuma ba a damu da a tsamo shi daga mugun kangin da aka wulla shi ciki ba da sunan bashi!.