Yanzu haka jami’an soji da ke karkashin rundunar sojojin Nijeriya, su sittin da takwas (68) su na fuskantar shari’a a gaban kotun soji kan zarge-zargen da suka shafi rashin da’a da dangoginsu a bataliyar sojin Nijeriya ta 8 da ke Sokoto.
Kwamandan bataliya ta 8, (GOC), Manjo-janar, Godwin Mutkut, shi ne ya shaida hakan a lokacin da yake gabatar da kara a gaban kotun da’ar sojoji da ke Sokoto ranar Juma’a, ya ce, an yi hakan ne domin tabbatar da da’a da ladabi a cikin aikin soji.
- Jirgin Yakin Sojin Saman Nijeriya Ya Tarwatsa ‘Yan Bindiga A Sokoto
- Kasurgumin Dan Bindiga Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayin Luguden Wutar Jiragen Yakin Sojin Sama A Zamfara
Ya kuma kara da cewa samar da kotun na da manufar hukunta jami’an da ke karya dokoki da ka’idojin aiki.
Ya ce, “Na gaji shari’ar daga wanda na karbi ragamar bataliyar nan a hannunsa, Manjo-janar Uwem Bassey, wanda aka masa sauyin wajen aiki zuwa Shalkwatar soji da ke Abuja.
“Kotun da’ar ta jagorantar rundunar sojin don ganin an gudanar da aiki bisa kwarewa da ladabi da biyaya. Sannan, tana jagorantar jami’ai wajen kara gogar da su da sanjn ka’idojin aiki.
“Kundin tsarin mulkin kasa da dokoki sun amince da kotun da’ar sojoji.”
Ya gargadi kotun da a kowani lokaci su kasance masu tsayawa a bayan gaskiya tare da tabbatar da gaskiya ga kowa ba tare da nuna son kai ko wariya ba, domin wanzar da gaskiya da adalci a kowani lokaci.