Akalla mutum daya ne aka tabbatar mutuwarsa yayin da wani guda kuma ya samu rauni sakamakon harbin bindiga da ake zargin daya daga cikin jami’an tsaro a tawagar dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (Mai ritaya) ya yi a kauyen Akuyam da ke karamar hukumar Dambam a Jihar Bauchi.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ‘yansandan Jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ga ‘yan jarida ya shaida cewar, “Abin da ya faru shi ne a ranar Litinin da karfe 8:30 na dare, dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar a lokacin da yake hanyarsa daga Dambam zuwa Akuyam domin yakin neman zabe, gab da shigarsu cikin Akuyam an kai farmaki ga tawagarsa.”
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum 2 Kan Zargin Sace Kananan Yara 2 A Kano
- Marwa Ya Sadaukar Da Karramawar LEADERSHIP Ga Buhari Da Jami’an NDLEA
Kamar yadda yake cewa, bayan harin da aka kai wa tawagar dan takarar APC din, daya daga cikin masu tsaro a tawagar ya bude wuta inda ya samu mutum biyu masu suna Saleh Garba (Dan shekara 35) da kuma Yakubu Yunusa (Dan shekara 20) dukkaninsu mazauna kauyen Akuyam kuma an kaisu zuwa asibitin FMC da ke Azare domin kulawar Likitoci.
Ya kara da cewa, “A ranar Talata muka samu tabbacin cewa daya daga cikinsu ya mutu a lokacin da yake amsar kulawar Likitoci. Tunin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, Aminu Alhassan ya bada umarnin a kaddamar da bincike kan lamarin. Ya yi addu’ar Allah ya jikan wanda ya rasu.”
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, a ranar 24 ga watan Nuwamba kwamishinan ‘yansanda ya gana da jam’iyyun siyasa inda ya nemi jam’iyyun da su gudanar da harkokin siyasarsu bisa kan ka’ida tare bin dokokin zabe gami da nemansu da su yi siyasa ba da gaba ba.
A bangarensu kwamitin yakin zaben dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, ya shaida cewar, ba su kai hari ga kowa ba illa ma su ne ‘yan adawarsu suka farmaka a kauyen Akuyam da ke karamar hukumar Dambam ya yin da suke cigaba da yakin zaben.
Da ya ke zantawa da manema labarai, daraktan yada labarai na kwamitin yakin zaben, Alhaji Salisu Barau, ya ce, duk da harin da aka kaddamar a kansu amma sun hana magoya bayansu maida martani domin kare rayuka da dukiya.
Barau ya kara da cewa an lalata musu motoci a kalla 15 zuwa 20 gami da jikkata wasu daga cikin mutanensu.
“Wasu mutane sun hau kan Bishiyoyi suna jifa da duwatsu dukka a kanmu. Mun samu mun tsira.”
Da aka tambayeshi ko su waye suka dauki nauyin harin, Barau ya shaida cewar, “Yan adawa ne suka dauka nauyin harin.” Da aka tambayeshi ko zai fayyace wasu ‘yan adawa ya sake nanata cewa dai ‘yan adawarsu ne.
“A fayyace yake ‘yan adawarmu ne suka kawo mana harin, saboda ba sai yiyu mu farmaki kanmu da kanmu ba.”
Ya cigaba da cewa, “Mun je Misa babu abun da ya faru illa ma dandazon jama’a da suka nuna mana kauna, Muna je Daraso, muka tsaya a Sade zuwa Hardawa dukka babu Wanda ya kai mana farmaki kuma ba mu farmaki kowa ba. Meye sa sai a Akuyam?.”
Da yake magana kan harin kuwa, Barau ya ce tun ma daren ranar Lahadi aka fara Kai musu harin a lokacin da suka yi kokarin shiga yankin Akuyam domin yakin zabe.
Ya tabbatar da cewa dan takararsu na gwamna mutum ne Mai son zaman lafiya da kwanciyar hankali don haka ba zai so kai ma wani ko wasu hari ba.