Mahukunta a kasar Faransa sun sanar da shirin haramta zukar taba sigari a wuraren shakatawa na bakin ruwa da sauran wuraren taruwar jama’a musamman wadanda ke kusa da makarantu.
Wannan dai wani yunkurin na dakile matsalar rasa rayuka sanadiyyar dabi’ar zukar taba sigari.
- Tinubu Zai Sake Karbo Sabon Bashin Biliyan 8.69
- NNPP Ta Nemi EU, Amurka Da AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano
An ruwaito cewa sun ce a duk shekara ana samun mace-mace dubu 75 masu alaka da taba sigari a sassan Faransa, dalilin da ya tilasta mahukuntan kasar daukar wannan mataki.
Manufar wannan doka a cewar mahukuntan shi ne tseratar da yaran da ke tasowa daga ta’ammali da tabar wadda masana ke ci gaba da gargadi game da illarta ga lafiya.
Nan da shekarar 2032 ne Faransa ke fatan kammala tsaftace jama’arta daga ta’ammali da taba sigari ta hanyar samar da yaran da za su taso daga yanzu zuwa wannan lokaci wadanda ba sa busa sigari.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta jima ta na zargin kamfanonin sigari da taka muhimmiyar rawa wajen gurbata muhalli baya ga haddasa asarar dimbin rayuka.