Ma’aikatar Wakafi da Harkokin Addinin Musulunci ta Kasar Kuwait, ta haramta wa limamai karanta Alkur’ani daga wayoyinsu na hannu a lokutan nafilfilun dare na watan Ramadan.
Jaridar Al Rai ta ruwaito cewa bayanin na kunshe ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun karamin minista mai kula da harkar masallatai, Salah Al Shilahi.
- Za A Fara Amfani Da Kyamara A Iran Domin Damke Mata Marasa Hijabi
- Yadda Ake Ittikafi Da Kuma Hukunce-Hukuncensa
Sanarwar ta karfafa wa limamai gwiwa da su rika amfani da haddarsu ta Alkur’ani a lokutan sallolin Tarawihi da Tahajjud, kasancewar su (limaman) misali ne ga sauran al’umma.
Ta kara da cewa ya kamata kowane limami ya yi muraji’ar karatunsa yadda ya kamata gabanin jan sallah a maimakon karantawa daga cikin waya.