Hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta sanar da haramta wa tankokin man fetur masu jigilar lita 60,000 zirga-zirga kan titunan Nijeriya, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025.
Matakin dai na da nufin dakile hadurran da tankokin dakon man ke yi, wadanda ke haddasa mummunar asarar rayuka.
- NNPCL Na Fuskantar Matsin-lambar Rage Farashin Mai
- Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000
Hakanan, daga kashi na huɗu na shekara ta 2025, babu wata motar dakon mai, wacce ke jigilar lita fiye da 45,000 da za a kara bai wa izinin dakon mai.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man.
“Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha.
An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa (NUPENG), hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki ta kasa (SON), DAPPRAMAN da NDPRAMAN.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp