Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da janye dokar hana fita da ta sanya sakamakon rikici da ya barke lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a jihar.
A ranar 1 ga watan Agusta, 2024 gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita bayan da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a fadin kasar t ta koma tarzoma a jihar.
- NIS Ta Fara Binciken Wata Mata Da Ta Yayyaga Fasfonta A Filin Jiragen Sama Na Legas
- Ba Mu Samu Umarnin Ƙara Alawus Ga ‘Yan Bautar Ƙasa Ba – NYSC
Wasu bata-gari sun yi amfani da zanga-zangar suka yi ta fasa kayayyakin gwamnati da na ‘yan kasuwa, lamarin da ya hukumomin jihar suka saka dokar hana fita.
An samu rahotannin ‘yansanda sun harbi wasu daga cikin mutanen da suka fito zanga-zangar ko da yake, ‘yansandan sun musanta hakan.
Bayan da al’amura suka fara daidaita a mataki na farko, an rage dokar wacce daga 8 na safe zuwa 2 na yamma.
Sannan daga baya aka sake rage dokar daga 6 na safe zuwa 6 na yamma.
A ranar Litinin hukumomi a jihar suka dage dokar baki daya, kamar yadda Kwamishinan yada labaran jihar, Baba Halilu Dantiye, ya sanar.