An tsinci jariri da ake zargin dan kwana biyu ne a duniya da aka yasar a harabar sansanin ‘yan gundun hijira a yankin Uhogia kusa da Benin, da ke Ovia a Jihar Edo.
Kodinetan da ke kula da sansanin, Fasto Solomon Folorunsho, ne ya sanar da hakan lokacin da ke gana wa da ‘yan jarida a ranar Juma’a, ya ce, jaririn ya na tsananin bukatar nonon shayarwa.
- Sudan: Jami’o’in Nijeriya Sun Sha Alwashin Bai Wa Daliban Da Aka Kwaso Guraben Karatu
- Bagudu Ya Gabatar Da Takardun Shaida A Kotun Sauraren Kararrakin Zabe A Kebbi
A cewarsa, wata da ba san ko wace ce ba ta yasar da jaririn a kofar shiga sansanin tare da rubutaccen sako a jikinsa a ranar Juma’a da misalin karfe 11 na safiya.
Ya ce yanzu haka jaririn na kan kulawar Likitoci a asibitin sansanin, “Mun gano jaririn dan kwanaki biyu ne da aka yasar a mashigar Sansanin dauke da sako a rubuce.
“Jaririn da aka yasar tare da rubutaccce sako da ke cewa ‘don Allah ku taimakeni ku kula da shi. Ba zan iya kulawa da shi ba ne, saboda bana da komai da zan iya ciyar da shi, kuma tabbas bana son kasheshi, don haka yanzu ya zama mallakinku don Allah’.
Kodinetan ya ce sun sanar da ‘yansanda, ma’aikatar kula da harkokin mata da DSS kan wannan lamarin.
Kazalika, Folorunsho ya roki mahaifiyar jaririn da ta fito don Allah ta bayyana kanta domin jaririn na tsananin bukatar shayarwa.
“Ina karfafar mahaifiyarsa da ta zo kada ta ji wani tsaro ta fito ta bayyana kanta domin yaron ya samu nonon uwa, in kuma hakan bai samu ba za mu nemi Madara a ke bayarwa yaro, don haka za mu nema musu tallafi.
“Ko kuma za mu san yadda za mu yi mu tara kudi mu kama wa mahaifiyarsa din gidan haya, mu taimaka da abincin da sauran kayan bukata, tun da ta ce dalilin yasar da jaririn kawai don ba za ta iya daukan nauyin yaron ba ne. To ta fito za a taimaka mata sosai.
“Na tabbatar idan da wannan tallafin mahaifiyarsa za ta kula da jaririn.”
“Amma idan mun yi duk mai yiyuwa hakan bai samu ba, za mu cigaba da kula da jaririn.”
Folorunsho, ya roki ‘yan Nijeriya da su taimaka wa jaririn da kayan sawa kayan abinci da sauran kayan da jariri ke bukata.